Dokar aiwatar da haraji ta Nijeriya da ake kira Nigeria Tax Administration Act (NTAA), 2025, ta wajabta mallakar lambar haraji da ake kira TIN ko Tax ID ga duk wanda biyan haraji ya hau kansa.
Wadanda haraji ya hau wuyansu su ne, ma'aikata, 'yan kasuwa da masu kirkira da fasaha da wadanda suke samun kudadensu a kasashen waje amma mazaunan wuraren da ake da hurumin karbar haraji a Nijeriya. Haka nan dukkanin kamfanoni da maaikatu da sauransu. Wadannan su ake kira Taxable Persons. Dokar ta ce ban da dalibai da marasa aikin yi da wadanda ba su da takamaimiyar sana'a ko aiki ko mukami.
Wanda biyan haraji ya hau wuyansa kuma ya ki mallakar TIN ko Tax ID da gangan, to ya aikata laifi kuma za a iya cin tararsa na kimanin dubu 50 a watan farko da dubu 25 a watannin gaba da bai yi TIN din ba.
To sai dai ba kamar yadda ke cewa ba, bankinka ba zai daina aiki ba don baka da TIN. Haka nan ba za a yi amfani da TIN domin a wawashe maka kudi a asusunka ba. Sai dai idan ka zo neman wani abu a gwamnatance, ana iya cewa sai da TIN ko Tax ID a lokacin ne kare zai kama gada. 😃
Domin mallakar TIN abu ne mai sauki, duk wata sabuwar rijistar CAC walau kamfani ko BN ko IT ko LLP na zuwa da TIN a makale jikin certificate din. Tsofaffin na baya ma suna iya samu idan
Ga daidaikun mutane kuwa, tsarin ya bayar da umarnin yin amfani da bayanan da ake da su a rumbunan NIN da BVN a ba su TIN dinsu. Wanda ya riga ya yi kuma ya wadatar.
A cikin tsarin da aka yi shi ne an umarci bankuna da sauran masu ruwa da tsaki da su aikawa da abokan huldarsu Tax ID bisa bayanansu da ake da shi na BVN. Kenan ba abin hanzari ba ne, da sannu kowa zai mallaka kuma ya biya haraji. 😃
A takaice dai wanda ba lallai ne ya yi TIN ba shi ne wanda ake kira Non-Taxable person. Watau dan makaranta, wanda ba shi da tartibiyar sana'a, mai zaman banza da kuma wanda bai zauna da kafafunsa ba watau wanda har yanzu gidansu ake ciyar da shi. Kuma ba abin gaggawa ba ne da sannu kowa zai samu nasa.

Comments
Post a Comment