Ponzi Scheme ya samo asali daga wani kwararren dan damfara dan asalin kasar Italiya, ana kiransa Charles Guglielmo Tebaldo Ponzi. An haife shi a shekarar 1882. Ya shiga kasar Amerika a shekarar 1903 da nufin ya yi arziki ya koma kasarsu kamar yadda ya ga wasu na yi. A shekarar 1910 ya yi wani laifi aka kama shi aka daure shekara daya. Bayan ya fito ya ci gaba da buge - buge har ya yi aikin banki wanda ke ba da kudin ruwa fiye da sauran bankuna. A wannan aikin ne ya fahimci irin dabarar da ake yi wajen diban kudin wani a biya wani da sunan riba ko bunkasar kudi.
.
Bayan bankin ya durkushe ya sake yin wata damfarar a kasar Kanada inda ya saci sa hannun wani mutum ya fitar da kudi daga banki. Aka kama shi aka daure shekara uku. Bayan ya fito sai ya gudu birnin Boston a kasar Amerika, inda ya auri wata mace 'yar asalin kasar Italiya.
.
Daga nan ya ci gaba da bubbugawa tsakanin karya da gaskiya har ya kafa wani kamfanin da ke tallata kayan mutane a jaridu da mujallu. A haka ne wani mutum daga kasar Spain ya aiko masa da wasika mai dauke da Kan Sarki domin ya bayar da amsa ta koma ga mutumin da hanzari. A wannna wasikar ne ya ga wata irin dama da babu wanda ya taba tunaninta. Ya ga cewar zai iya saro irin wannan Kan Sarkin daga wata kasa ya sayar a Amerika, karshe ya samu riba misalin ninki hudu na uwar kudinsa. Da ya samu wannan dabara sai kuma ya shiga tunanin inda zai samu jarin da zai soma wannan kasuwanci.
.
Duk bankin da ya je neman rance sai su hana shi, wani karamin banki mai suna Hanover Trust ma har korar kare suka yi masa. Ya rika manyan attajirai neman bashi bai samu ba. Bayan wani lokaci sai ya tuna da dabarar nan da ya ana yi a bankin nan da ya taba rike mukamin Manaja. Ya soma neman masu zuba hannun jari da zummar zai biya mutum kashi 50 tare da uwar kudinsa bayan kwana 45. Idan kuma kudin sun kai kwanaki 90, zai biya kashi 100 a matsayin riba.
.
Mutane da suka ji garabasa sai suka yi ta kawo kudi suna zuba hannun jari. To amma sai lamarin da ya yi tsammani wajen cinikin Kan Sarki ya zo masa da ba zata. Domin ba a cika nemansa sosai ba, kuma ba shi da yawan da za a dogara da shi a matsayin sana'a tabbatacciya. Duk da haka Ponzi ya ci gaba da rudin mutane da cewa ya gano abin da babu wanda ya gano. Aka yi ta zuba hannun jari, tun daga lissafin kwabo har ya zarce zuwa malala gashin tunkiya. Duk wanda ya zuba hannun jari sai a bukaci ya je ya nemo wasu karkashinsa su ma su zuba jari, shi kuma a kara masa da tukuici. Idan lokacin biyan kudin ya yi, sai a lallabi mutum a biya shi rabi, ragowar kuma a ce ya bari su kara kauri.
.
Mutane suka yi ta sayar da kadarorinsu suna kawowa Ponzi yana kalmashewa. Cikin kankanin lokaci ya tara kudi masu dumbin yawa. Ya sayi wata irin mota da ake yayi a wannan lokacin mai suna Locomotive. Har ila yau kuma ya sayi wani katafaren gida mai girman kilomita biyu. Daga bisani saboda yawan kudin da asusunsa ke da shi a bankin Hanover, tilas suka amince ya zama shugaba kuma babban darakta a bankin.
.
Saboda yawan kudin da ake ta lafta masa kullum da yadda labarinsa ya watsu kamar wuta daji, ya sa hukumomi suka soma sa ido a kansa, to sai dai kuma hatta 'yansanda da alkalai da sojoji sun zuba hannun jarinsu a wajensa. Don haka aka rasa yadda za a yi da shi.
.
Rahoton da kwakkwafi da jaridar Boston Post ta yi wanda ta gano asalinsa da irin rayuwar da ya yi a baya, ya sa jama'a suka shiga shakku game da shi. Nan fa aka yi ta zuwa ana fitar da kudi. Aka yi ta fitarwa har zamana asusun bankinsa da ke dauke da kudi malala gashin tunkiya ya zama babu ko karfanfana sai lodin bashi da ake kira 'Overdraft'. Bankin Hanover suka ga alamun sun dauki hanyar durkushewa saboda fitar da kudin da ake yi ba kakkautawa, sai suka ciro hannun jarin Ponzi da ke wajensu na dala miliyan 1.5 suka kwashe abin da suke binsa bashi na dala dubu 500, sannan suka dauke kudin ruwa suka ba shi abin da bai wuce dala dubu 400 ba. A lokacin kuwa an kiyasta cewa ana binsa bashin dala miliyan 7.
.
Matar Ponzi mai suna Rose Maria da ta ga abin ya wuce hankali, sai ta tursasa masa ya mika kansa ga hukuma. Aka caje shi da laifuka goma sha daya kowanne ya kunshi hujjoji sama da 120. Bayan an jima ana fafatawa da shi, matar ta sake matsa masa ya amsa laifinsa. Aka daure shi shekara bakwai. Bayan ya fito kuma aka sake kama shi bisa laifin kwace aka daure shi shekara biyar. Daga nan aka tasa keyarsa zuwa kasarsu.
.
Ja'irin sai ya waske, ya ki zuwa kasarsu ya tafi jihat California, acan ma ya kafa irin wannan kasuwanci da sunan 'Cinikin Fuloti mai riba'. Duk wanda ya kawo kudinsa za a ba shi ninki 2 bayan wata uku. Babu jimawa gwamnatin jihar ta damke shi aka daure shi shekara biyu. Yayin da ya fito sai aka gano ashe ma ba shi da shaidar zama dan kasa duk zamansa a Amerika kusan shekara 30. Nan da nan aka iza keyarsa zuwa kasarsu. A can ma dai ya rika taba irin wannan sana'a ba tare da nasara ba. Karshe ya tafi Birazil ya mutu a wani asibitin gajiyayyu da ke birnin Rio de Jeneiro a shekarar 1949.
.
Saboda shaharar da macucin nan ya yi, ya sa ake kiran irin wannan sana'a da sunansa watau Ponzi Scheme. Har yanzu ana samun wadansu na amfani da irin wannan dabara wajen dulmiyar da dukiyar mutane ta hanyar nuna musu wani irin nau'in kasuwanci mai riba. Amma a zahirin gaskiya kudin wasu suke diba suna biyan wasu, a karshe dole sai an samu wanda ba zai samu kudinsa ba har abada.
.
Daga mashahuran macutan da suka yi kaurin suna a irin wannan sana'a bayan Charles Ponzi kuma akwai Barnie Madoff wanda yanzu haka an daure shi tsawon shekara 150. Sai kuma Sergey Mavrodi, dan asalin Rasha wanda yanzu yake cin karensa babu babbaka anan Nijeriya. Mutane suna ta zuba hannun jari da sunan gudunmawar juna.
.
Rubutu na gaba zan kawo tarihin wadannan shahararrun 'yan damfarar.
Comments
Post a Comment