ADO BAYERO: JARUMI CIKIN JARUMAI
Shekaru hamsin da daya kenan da nadin mai martaba marigayi sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero. Kuma an mika masa sandar sarauta a cikin watan Oktoba na shekarar 1963, wannan ya biyo bayan rasuwar mai martaba sarki Muhammadu Inuwa wanda ya sarauci Kano tsawon wata shida kacal.
A tsawon wadannan shekaru, marigayi Ado Bayero ya yi fadi tashi da gwagwarmaya da nuna halin juriya da dauriya da tawakkali a lokuta da dama cikin mabambamtan abubuwa. Ya yi mulki da gwamnoni goma sha tara, sojoji goma sha hudu, farar hula biyar. Ba domin jarumi ne ba, ba domin hakurinsa da iya siyasar sa ba da bai tafi da kowa lafiya.
Shekaru hamsin da daya kenan da nadin mai martaba marigayi sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero. Kuma an mika masa sandar sarauta a cikin watan Oktoba na shekarar 1963, wannan ya biyo bayan rasuwar mai martaba sarki Muhammadu Inuwa wanda ya sarauci Kano tsawon wata shida kacal.
A tsawon wadannan shekaru, marigayi Ado Bayero ya yi fadi tashi da gwagwarmaya da nuna halin juriya da dauriya da tawakkali a lokuta da dama cikin mabambamtan abubuwa. Ya yi mulki da gwamnoni goma sha tara, sojoji goma sha hudu, farar hula biyar. Ba domin jarumi ne ba, ba domin hakurinsa da iya siyasar sa ba da bai tafi da kowa lafiya.
A shekarar 1966 aka yi juyin mulki na farko wanda a ciki aka rasa rayukan wasu manya daga shugabannin Nijeriya wadanda suka hada da Marigayi Abubakar Tafawa Balewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da sauransu. Wannan abu ya daga hankalin mutane musamman a Kano, inda komai ya tsaya cik aka rinka yada jita - jitar an kama sarakunan gargajiya ciki har da mai martaba sarki Ado Bayero. An ruwaito cewa Ironsi ya tattara sarakuna gaba dayansu a Ibadan da nufin a sanya musu bom a dakin taron gaba daya su mutu, babu wanda ya tunkari Ironsi kai tsaye sai marigayi Ado Bayero, wanda a lokacin Ironsi ya karyata wannan zance. A Kano kuwa an shiga rudani musamman rashin sanin halin da sarakunan ke ciki. Bayyanar mai martaba sarki cikin jama'a yana hakurkurtar da su domin hankulansu ya kwanta a zauna lafiya. Wannan jawabi na mai martaba ya sa hankula sun kwanta an samu nutsuwa.
Kafin komai ya warware, hankula su kwanta, sai kuma yakin basasa ya tashi. Wannan yamutsi ya haifar da asarar rayuka, an kashe mutane babu iyaka, haka nan an yi asarar dukiya ta fi gaban lissafi. Irin wannan lokaci mai tsananin wahala mai martaba sarki ya jajirce wajen wayar da kan jama'a da a zauna lafiya. Wannan kokari ya sa tsananin yakin bai shafi Kano sosai ba. Sarki ya zama shugaban Kanawa kuma sarki a jihar Kano wadda aka kirkiro a shekarar 1967. Duk da jihar Kano tana karkashin gwamna ne, amma mutane ba su damu da kai kara ko koke ga gwamnati ba sai wajen sarki.
A shekarar 1976 wasu kananan hafsoshi suka kashe shugaban kasa Janar Murtala wanda ya ke dan asalin jihar Kano ne, mutane sun shiga rudani sun shiga zullumi a dukkan fadin kasar nan. Daliban jamia na wancam lokacin suka tattaru a jamiar Ahmadu Bello Zariya suka taho Kano a kasa domin halartar jana'izarsa. Suka sha alwashin ko za a yi ha maza ha mata sai sun dauki fansar wannan kisan da aka yiwa shugabansu. To amma shiga tsakani da mai martaba ya yi, da zuwan da ya yi filin saukar jirage ya karbi gawar da jawabin da ya rika yiwa jama'a ya sa hankula suka kwanta, aka samu daidaito a wannan lokaci mai matukar wahala. Ba domin an samu jarumin shugaba ba, da hakan bai samu ba. Allah ne kadai kuma ya san yawan rayuka da dukiyar da za a rasa.
Dawowar mulkin siyasa a karo na biyu, watau jamhuriyya ta biyu, ya zo da wani juyi na musamman mai wahala wajen tafiyar da mulkin al'umma. Da farko dai kundin tsarin mulki ya kassara tasirin sarakuna wajen sha'anin mulki, sannan an halastawa kowa ya shiga takarar mukami komai cancantarsa ko akasin haka. Wannan ya sa aka samu shugabannin da ba su mutunta sarakai kuma suke tilasta musu wasu ra'ayoyin da ba nasu ba. An samu hautsinin rikicin addini wanda Mai Tatsine ya jawo a wasu sassan arewacin kasar nan, inda aka kashe mutane aka lalata dukiyoyi masu dimbin yawa. Wannan ya jawo matsalar durkushewar tattalin arzikin jihohi da dama ciki har da Kano inda anan abin ya fi tsamari. Haka nan sabanin da ya auku tsakanin masarauta da gwamnatin jiha ya jawo asarar rayuka inda aka kone gidan rediyon Kano da wasu ma'aikatun gwamnati. Haka kuma aka hallaka wasu jami'an na gwamnati. Duk wannan abin da ke faruwa, mai martaba sarkin Kano bai zama ya raina matsayin da ya tsinci kansa ba, ya yi hakuri ya gyara tsakaninsa da gwamnati, ya zauna da su lafiya har aka kammala jamhuriyya ta biyu, mulkin soja ya sake dawowa.
Sojoji ba su tsame hannunsu ga sha'anin sarautar Kano ba, sai da ta kai an hana sarki fita waje saboda wasu dalilai, amma duk da haka bai kawar da kansa ga barin mutanensa ba, a kullum mutane sai dada tururuwa suke yi zuwa gare shi domin yin alkalanci da neman shawara da neman taimako da sauransu. Duk kuwa da cewa tuni an janye hannun sarakuna daga shiga harkokin mulki da hukunci. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba daga irin kwarjini da girma da jama'a ke yiwa sarkin ba.
Haka nan Kano ta sake aukawa cikin wani rikicin musamman akan nuna adawa da zuwan wani malamin addinin kirista mai suna Reinhard Bonke a shekarar 1991. Irin gudunmawar da mai martaba ya bayar wajen kwantar da hankula babu shakka abin yabawa ne.
Jarumtakar sarki ta sa bai taba juya baya bisa manufar abin da ya sa gaba ba, ya taka rawa sosai wajen tafiyar da zaman lafiya a jihar Kano. Dukkan tashin hankalin da ya auku a Kano cikin shekara ta 2000 da ta 2004 da kuma 2012.
Irin wannan jarumtaka ba kowanne mahaluki ake samu da shi ba, babu shakka marigari mai martaba Ado Bayero ya bar duniya a cikin nasara. Inda ya bar ta a cikin dakinsa kwance cikin lumana babu hayaniya babu walagigi. Sarki marigayi Ado Bayero bai zama mai kasala ba, duk inda aka gayyace shi kuma ya amsa zai je bai taba latti ba, babu zancen makara a wajensa.
Sarki ya bar duniya ranar Juma'a, ranar da aka hakikance wanda ya bar duniya a cikinta yana tare da rahamar Allah. Sarki ya samu dimbin dubunnan jama'a sun halarci sallarsa, wanda hadisi ya tabbatar da yawan jama'ar da suka halarci sallar mutum alamar samun rahamar Allah ne. Mai martaba ya samu shaida ta gari daga jama'a da dama wadanda suka hada har da magautansa.
Muna yi wa marigayi mai martaba kyakkyawan zato tare da fatan Allah ya rahamshe shi. Allah ya sadar da shi Annabin Rahma. Ubangiji ya jibinci bayansa, mu kuma kanawa Allah ya ba mu wani shugaba adali nagari wanda zai kwatanta wasu daga halayen marigayi musamman na hakuri da jarumta.
-Danladi Haruna. 06 - 06 - 2014
Comments
Post a Comment