Sabuwar dokar haraji da ake sa ran za ta soma aiki a sabuwar shekara mai zuwa ta 2026 a Nijeriya ta zo da wasu tanade-tanade da hukunci ga duk wanda aka samu da aikata ba daidai ba.
Ita dai wannan doka ta hada nau'ikan haraji daban daban da a baya ba doka daya ce ke gudanar da su ba. Misali, akwai dokar biyan haraji daga kudin aunaka watau PAYE, da dokar harajin ribar kamfanoni watau CIT da dokar karin haraji akan kayan masarufi watau VAT da dokar kudin ladan gaɓe watau WHT da kuma dokar harajin sayar da tsoffin injina watau CGT da sauransu. Duka wadannan dokokin an dunkule su waje guda a wannan sabuwar doka domin saukin fahimta da saurin aiwatarwa.
Akwai wasu abubuwa da mutane ya kamata su gane musamman wajen laifuffuka da hukuncinsu domin gujewa da kiyayewa. Wasu daga dokokin su ne kamar haka:
1. Kin yin rijista akan lokaci. Idan kamfani ya ki yin rijista da hukumar tattara haraji a lokacin da ya dace, to za a ci shi tarar dubu 50 a watan farko sannan ragowar watannin kuma dubu 25 kowanne. Ana so kamfani ya yi rijista da hukumar tattara haraji a cikin wata 6 da soma aikinsa. Misali, kamfani ya soma aiki a Janairu, wajibi ne ya yi rijista da hukumar kafin Yuni. Idan ya sake ya zarce hakan, to tarar dubu 50 a watan Yuli, dubu 25 a Agusta har zuwa dai lokacin da zai je ko aka tilasta masa yin rijistar.
Wanda ya ba wa kamfani mara rijista da hukumar tattara haraji ko mutumin da ba shi da lambar haraji ta TIN ko makamancinta, to ya aikata laifi na tarar miliyan 5 ko sama da haka.
2. Kin kai bayanin kudin VAT: Idan mutum ko kamfani suka ki kai bayanin VAT, to za a ci tarar dubu 100 a watan farko sai kuma dubu 50 kowanne wata. Bayanin VAT zai zo a wani rubutun.
3. Kin bayyana sauran haraji: Idan mutum ko kamfani suka ki kai rahoton sauran bayanai to akwai tara ta dubu 50 ga mutum ko dubu 100 ga kamfani.
4. Rashin ajiye sahihan bayanan kasuwanci. Idan kamfani suka kasa ajiye sahihan bayanai dangane da harkokin kasuwanci ko aikin da suke yi, za a ci tarar su dubu 50. Idan aka ce su kai bayanan cinikinsu kuma ba su iya kaiwa a ranar da aka ce ba, to za a ci tarar su a rana ta farko dubu 200, sannan kowacce rana kuma dubu 10 har sai sun kai takardun da ake bukata. Nan gaba zan yi bayani akan abin da ake kira Tax Audit, Returns and Investigation.
5. Rashin amsa Takardar Bukatar Biyan Haraji (Demand Notice)
Idan jami'an haraji suka kawo maka takardar biyan haraji, wajibi ne ka bayar da amsa walau ka amince ka biya kudin da aka rubuta a jiki watau Compliance, ko kuma ka nuna rashin amincewarkana rubuce watau Objection. Idan ka gaza daya daga wadannan, to akwai tarar dubu 100 a ranar farko da kuma dubu 10 kowacce rana har sai ka yi abin da ya dace.
6. Rashin yarda a saka na'urar bincike a kamfani ko wajen sana'a. Idan gwamnati ta makala maka na'urar ko inji ko ma'aikatan da za su saka ido ga aikin da kake yi kana samun kudi, (ana maganar kamfani ne anan), sai ya zamana an hana wannan abin aiki da gangan ko an ki yarda a makala shi inda ya dace. To akwai tarar miliyan 1 a ranar farko, sannna kowacce rana akwai tarar dubu 10 har sai komai ya daidaita. Wadannna na'urori ko ababe ana kiransu Fiscal Tools. Bayaninsu zai zo nan gaba.
Haka nan duk wanda aka makalawa Fiscal Tools din nan kuma ya ki amfani da su yadda aka yi umarni, to akwai tarar dubu 100 sannan harajin da zai biya za a ninka shi sau 100% har ila yau da kudin ruwa bisa adadin da aka lissafa.
7. Kin cire harajin ladan gaɓe - WHT
Idan kamfani ya yi kwangila, ana cire masa wani kudi da sunan Withholding Tax. Wanda daga bisani zai iya amfani da shi wajen biyan haraji. Idan kamfanin da ya bayar da kwangilar ya ki cire wa, ko bayan ya cire ya ki kai wa hukuma, za a ci tilasta ya kai kudin nan tare da tarar 10% da kuma kudin ruwa.
Idan ma kudin da yawa ana iya hadawa da daurin shekara 3 da tarar 50% na ainihin kudin da ya kamata ya kai.
8. Cin Mutuncin Ma'aikatan Haraji
Zagi ko cin mutunci ko wulakanci ko duka ko raunata ma'aikatan tattara haraji a bakin aikinsu laifi ne mai girma a wannan doka. Za a iya daure mutum shekara 10 babu tara.
Haka nan nuna makami da barazana ga ma'aikatan tattara haraji akwai daurin shekaru 5.
Idan kuma aka samu mutum ko kamfani da laifin kokarin ba wa ma'aikatan cin hanci ko toshiyar baki, tarar dubu 500 ga mutum ko miliyan 2 ga kamfani da daurin shekara uku da kuma tilasta a biya harajin da aka lissafa.
9. Dokar Kirifto da Masu Kula da Digital Assets
Biyan haraji ga ribar Kirifto wajibi ne a wannan doka kuma dole masu kula da shi da ake kira Virtual Asset Service Providers (VASPs) su bi ka'idojin da aka gindaya musu. Rashin yin hakan yana jawo a ci tarar su naira miliyan 10 a watan farko sai kuma duk wata miliyan 1 har sai sun yi abin da ya dace. Idan sun gaza kuma za a iya kwace lasisinsu gaba daya.
10. Laifuka a Harajin Stamp Duty
Idan kamfani ya ki biyan kudin sitamfi, za a ci tarar sa na 10% da kuma kudin ruwa. Sannan akwai tarar dubu 100 ga kamfanin da ya kasa bayyana kudin sitamfi. Idan ya boye wani abu kuma, ana iya yi wa shugabanninsa daurin shekara 3 da horo mai tsanani.
11. SOJAN GONA
Duk wanda aka samu da laifin yin karyar cewa shi ma'aikacin tattara haraji ne, za a ci tararsa Naira miliyan 1 da daurin shekara 3. Haka kuma duk wanda aka samu da hadin baki wajen tauyewa ko lalalatawa ko jingine biyan haraji, to za a ci tararsa Naira miliyan 1 ko daurin shekaru 3.
********
Wasu hukunce - hukuncen dama can akwai su, sai dai an sabunta su tare da kara musu horo ne. Wasu kuma sabbabi ne domin dakile abin da ake kira Tax Evasion.
Don haka, ina shawartar duk wanda dokar nan za ta shafa, Kamfanoni, Ma'aikata, Hukumomi, 'Yan Kasuwa, 'Yan Siyasa, Jami'an Tsaro da sauran jama'a, da cewa kada su yi abu da ka. Su tabbatar sun samu wadanda suka san harkar haraji sosai domin jin shawarar su da dabarun da za su yi domin samun sauƙin kudin haraji da samun saukin biya a sannu sannu.
Danladi Haruna, ACA, ANCS




Comments
Post a Comment