Mutane na ta himmar habaka Business Name dinsu zuwa Company domin dabarar suke zaton za ta fisshe su wajen samun rangwamen kudin haraji. Da farko dai Business Name da ake ba shi lamba mai farawa da BN da kuma Kamfani da ake ba shi lamba da ke farawa da RC, duka a halin yanzu ana ba su lamba da ke farawa da RC ne. Kenan ta nan duka dangatakarsu daidai.
Ba dabara ba ce ka mayar da Business name zuwa Company saboda tunanin sai ka yi cinikin miliyan 100 za a soma cajinka haraji. Bal ma dai, karawa gwamnati kudi ka yi maimakon rage mata.
Mu fahimci cewar dawainiyar kamfani ta fi ta Business Name ta wajen sarrafawa da alkintawa musamman ga irin kasuwancinmu na daga ni sai 'ya'yana, daga buhu sai tukunya. Kudaden da ake kashewa a hukumance da zirga-zirgar da ake yi da rikita-rikitar da ake warwarewa kafin kamfani ya zauna da kafafunsa ya ninka na Business Name nesa ba kusa ba. Wata ran za mu kawo wasu daga cikin ababen.
Idan ka ce ai hujja shi ne sai ka samu cinikin da ya kai naira miliyan 100 sannan za a yi maganar haraji, to ka sani kamfani yana biyan haraji iri - iri kamar haka:
VAT: shi ne harajin da kayayyakin masarufi da ake ɗiba daga cinikin da kamfani ya yi ko aka yi masa. Kodayake, Business Name ma yana biyan VAT amma akwai irin VAT da ake input da output wadanda ba lallai ne kai karamin dan kasuwa ka biya input ba. Wanda ya ki biyan kudin VAT akwai tara da daurin shekaru uku.
Development Levy: A sabuwar doka an hade harajin Education Tax, da Police Fund Tax, da NITDA da Development levy zuwa 4% na abin da ake kira 'Assessible Profit'. Dole kamfani ya biya wannan. Business Name kuwa ba ruwansa.
Baya ga wannan wasu ababen da ake bukata ga kamfani sun hada da:
a. Ajiye sahihan bayanan ciniki wanda kuma a kowanne lokaci hukuma na iya tambayar har na tsawon shekaru 6 watau Back Duty Assessment. Idan babu to ka yi laifi, shi ma tara ce da dauri kamar yadda na ambat a rubutun baya.
b. Duk shekara sai ka je hukumar ka yi bayanin cinikin da ka yi da yadda ka yi watau self assessment and returns. Rashin yin hakan laifi ne mai dauke da tara da dauri ko duka biyun.
c. Wajibi ne ka amsa gayyatar da hukumar tattara haraji za ta yi maka a duk lokacin da aka bukaci hakan. Rashin amsa gayyata laifi ne. Ka ga a BN duk ba ka da wannan rigima.
d. Mai Business Name yana hulda da hukumar tattara haraji ta jihar da yayi rijista ne. Don haka WHT da PAYE duka nan zai biya. WHT ba ya wuce 5%.
Kamfani kuwa yana hulda ne da hukumar tattara haraji ta kasa. Idan sun ga dama sai su kai maganarka zuwa Abuja ko Legas ka yi ta sintiri idan kana neman wani abu. Haka kuma WHT na kamfani 10%.
Idan ka lissafa dawainiyar assessment da returns da Compliance da DVT za ka ga kudin da za ka barnatar sun fi wanda za ka biya na PAYE a karkashin BN.
Duka wadannan ababen dubawa ne kafin ka habaka rijistar BN dinka zuwa kamfani matuƙar dai ba wasu daraktoci za ka kara ba ko kuma shigo da masu hannun jari watau shareholders.
Don haka, mai son mayar da BN dinsa zuwa RC ya soma tuntubar masana abin gwargwadon kasuwancinsa kafin daga bisani ya dawo yana cizon yatsa.
Wasallam
Danladi Z. Haruna ACA, ANCS

Comments
Post a Comment