Hukumar zaɓe ta ƙasa ce ke da alhakin aiwatar da kiranye kamar dai yadda take gudanar da zaɓe. Kiranye shi ne dawowa daga rakiyar wakilcin zaɓaɓɓen ɗan siyasa ke yi wa al'ummarsa. Zaɓaɓɓen ɗan siyasa shi ne wanda ya yi nasara a zaɓen ƙarshe da aka gabatar a yankin da yake wakilta.
Kundin tsari mulki na ƙasar Nijeriya sashi na 69 da na 110, kazalika da dokar zaɓe ta 2022 sashi na 116 ne suka ƙarfafi hukumar
zaɓe ta ƙasa da ta gudanar da kiranye ga 'yan makali jiha ko na tarayya gami fa shugabannin ƙananan hukumomin birnin tarayya Abuja. Da zarar hukumar ta INEC ta karɓi rubutacce kuma halastaccen ƙorafi daga al'ummar yankin da wakilin yake, sai ta shiga haramar aiwatar da kiranye.
HALASTACCEN ƘORAFI
Ba kowanne ƙorafi ne halastacce ba a fuskar doka. Wajibi ne ƙorafi ya zama a rubuce. Kuma daga al'ummar yanki waɗanda suke da katin zaɓe. Sannan wajibi ne a samu kashi 50 cikin na mamallakan ƙuri'a sun saka hannu a takardar ƙorafin. Watau misali, idan yankin mazaɓar Daddarawa na da rijistar masu zaɓe dubu goma, to sai dubu biyar sun saka hannu akan ƙorafin kafin ya zama halastacce.
MIƘA ƘORAFI
Idan masu korafin sun shirya, suna iya 'tunkarar hukumar zaɓe domin ta ba su kwafin amintattun masu riƙe da ƙuri'a watau Certified True Copy. Da zarar an ba su kwafin sai su soma tattara sa hannun jama'a har a samu adadin da ake so.
Idan an kammala saka hannun sai a miƙawa hukumar zaɓe, ita kuma za ta yi nazari da tantance sahihancin bayanan. Idan hukumar ta gano akwai kuskure ko kuma wata ƙa'ida bata cika ba, sai a jawo hankalin al'ummar domin su gyara. Idan ba su gyara ba sai a jingine batun har sai sun cika dukan ƙa'idojin.
TANTANCEWA
Idan kuma ƙa'idojin duka sun cika sai a saka ranar tantancewa watau Verification.
Tantancewa iri biyu ce. Irin na farko ana kiranta Recall Verification, watau masu zaɓen da suka saka hannu su fito su jaddada cewar lallai su ne suka amince a yi wa wakilinsu kiranye. Wajibi su kai aƙalla kashi 50 na masu rijista a yankin ko sama da haka.
Nau'i na biyu kuma ana kiransa Referendum Recall watau dukkan jama'ar yanki baki ɗaya su fito su kaɗa ƙuri'ar EH ko A'a ga wakilinsu. Wajibi ne masu EH su kai kashi 50 na masu kaɗa ƙuri'a ko fiye da haka kafin kiranyen ya tabbata.
Idan adadin bai kai yadda aka ambata ba, sai hukuma ta sanar da cewa ba a yi nasarar kiranyen ba, amma masu ƙorafi na iya sake aiwatar da wani kiranyen yadda za su yi nasara.
TSAWON LOKACI
Daga ranar da hukumar zaɓe ta karɓi ƙorafi zuwa kammala komai da komai, tilas ne a ƙarƙare shi cikin kwanaki 90. Idan an haura hakan, an shiga wani abu kuma. A tsakanin wannan lokacin, masu ƙorafin na iya janye wa su ƙyale wakilin nasu ya yi ta yi. Kowanne wakili shi ɗaya za a yi wa kiranye. Ba a haɗa wani da wani.
Misali, ba za a iya yin ƙorafin akan ɗan majalisar Amarawa da na Kyakyatawa a korafi guda ba. Haka nan ba a haɗa korafi kan ɗan majalisar jiha da na tarayya a waje guda ba, ko kuma a hada su da na sanata ba. Kowa mazabarsa daban watau Constituency.
Idan ranar yin zaben na raba gardama ta zo, kowa akwatinsa za shi ya bayyana ra'ayinsa watau ko dai ya tabbatar da sa hannunsa ko kuma ya jefa kuri'ar EH ko A'a.
SAU NAWA KIRANYE YA YI NASARA?
A sani na tun daga 1999 zuwa yau, an jarraba yin kiranye kamar na George Okoye, Simon Lalong, Dino Malaye, Farouk Adamu Aliyu da Umar Jibril. Duk waɗannan yunƙuri an yi an gama ba yare da nasara ba duk da ƙarfin tuwon da gwamnoni suka nuna a yunƙurin.
Don haka masu shirin yi wa wakilansu kiranye kofa a bude take amma fa ba ta ɓullewa.
- Danladi Z. Haruna
Zan dawo na karanta daga baya.
ReplyDelete