Ƙagaggen Labari daga Danladi Haruna
Gari ya waye, hasken rana ya baje bisa doron ƙasa da gidaje cikin launin ruwan zinariya. Wannan yanayi ya dace da irin shigar da sabon Matawalle ya yi. Da ganinsa ka ga alamun yau rana ce ta musamman. Ya caba ado da wata irin babbar riga mai aska goma sha biyu, wadda aka yi wa aikin tsamiya na asali.
Hasken da ƙyalƙyalin da rigar ke yi kaɗai ya isa abin kallo. Dokinsa ma an caba masa ado irin na sarakuna, yana tafiya cikin takama tamkar dai yana jin abin da maroka ke fada.
Biye da Matawalle, makada ne da mawaka ke ta kida wani ba ya jin na wani. Sai dai busar algaita ce ta fi ratsa kunnuwansa musamman da ya ji mai algaitar yana cewa da shi, "Toron giwa da toron giwa. Matawalle ka fi gaban raini!"
Maroka kowa na fadin albarkacin bakinsa irin zugar da yake yi masa. Marokin da aka fi jin amon sautinsa cewa yake, "ga dodo maci wani dodon. Ga zaki karya barage. Ga kura uwar karnuka. Kai arna ku gafara Matawalle nadin Allah!"
Matawalle na jin irin wannan kirari, sai ya rika jin wani kumburi na ratsa sassan jikinsa. Ya ji kamar kasa ma ba za ta iya daukarsa ba. Ya rika jan linzamin dokin suna tafiya sannu. Hagu da dama mutane ne tsaitsaye suna jinjinar ban girma. Yau dai matawalle ya zama Matawalle!
Cikin ransa cewa yake yi, "wai! Ashe haka sarauta take da dadi? Da na sani ai da tun a tsohuwar masarauta zan nema saboda ta fi nan kwarjini. Sai dai kuma acan zan jima kafin na samu saboda yawan manema."
Aka karasa kofar fada, Sarki da kansa ya taso ya tari Matawalle. Aka shiga cikin fada kowa ya zauna a mazauninsa. Daga nan wani bafade ya dauko wani rawanin zawwati da jar dara ya shiga nannadawa sabon Matawalle.
Da aka gama nadin Sarki ya gyara zama domin gabatar da jawabi. Ya ce, "Matawalle na farko a wannan masarauta, muna taya ka murna iri biyu. Na farko ga shi ka gama aikin gwamnati lafiya. Na biyu ka dace da samun sarautar Matawalle a wannan lokaci. Muna maka fatan alheri. Da fatan ka gama lafiya."
Sarki ya ja numfashi ya dubi morinsa ya ce, "a bamu waje mu gana da Matawalle." Mutane suka rika fita daya bayan daya har ya rage sauran hadiman Sarki kadai da sabon basarake. Sarki ya dubi Matawalle ya ce, "abin da nake so na shaida maka shi ne, sanin kanka ne wannan masarauta jaririya ce, tana bukatar gudunmawa daga gogaggun mutane irin ku." Matawalle ya gyada kai ya ce, "lallai kam hakika a shirye nake wajen bayar da gudummawata domin cigaban wannan yanki."
Sarki ya ce, "madalla da kai. To abu na farko dai ka sani ba ma bayar da albashi a masarautar nan saboda har yanzu bamu samu cikakken iko ba sai abinda ba a rasa ba." Matawalle ya gyada kai.
"Shi yasa ma muka ga dacewar jawo ka a jiki domin ka taimaka mana tunda ka gama aikin gwamnati lafiya, lallai kana da kudin da za ka tallafa mana." Matawalle ya dubi sarki cikin rashin fahimta ya ce, "Allah baka nasara, ayi min karin bayani."
Sarki ya ce, "abin nufi za mu yanka maka haraji ko alawus da za ka rika kawo mana duk wata gwargwadon girman sarautar ka a wajenmu. Sannan za mu ba ka hayar dawakai da bayi da sauran kayan sarautar da kake bukata. Wannan zai kara mana hanyoyin kudaden shiga."
Matawalle ya ji wani abu ya sauko makogwaronsa ya tokare. Ya yi yunkurin hadiyar yawu ya kasa.
Muryar Sarki ta doki kunnuwansa yana cewa, "abu na gaba, bamu yarda ka yi kowacce irin mu'amala da kowacce masarauta ba sai da saninmu." Cikin sauri Matawalle ya ce, "kowacce irin mu'amala? Ina da mutane da dama acan da yanzu haka suka zo mini caffa. Matana ma daga can suke."
Sarki ya ce, "idan akwai lalura, za mu iya ba ka dama amma za ka biya kudin fito gare mu. Ta haka za mu bunkasa har mu yi gogayya da kowacce masarauta. Tashi na sallame ka." Fadawa suka amsa gaba daya, "godiya yake!"
Matawalle ya fito fuskarsa murtuk kamar kunun kanwa ya sha iska. Maroka na ganinsa sai suka goce da kida. Maroka na zarya suna kirari. Algaita na feshi tana cewa, "Babba uban babba. Ga babba wanda ya fi babba!"
Maroki na ta wasa Matawalle yana cewa, "Zaki uban giwa da kura. Zarto karfe maci karafa! Gizago sha wafce!" Shi kuwa Matawalle cikin ransa sai ya ji kamar zaginsa suke yi. Ya ji rigar nan ta yi masa nauyi musamman idan ya tuna harajin da za a lafta masa b gaira ba dalili alhali yanzu ban da dan fanshon da za a rika jefa masa ba shi da wata hanyar samu. Ya dubi maroka da makada da dumbin al'ummar da ke biye da shi sai ya ji ransa ya yi bakikkirin. Ya ji kamar ya sauka daga dokin ya tafi gida a kasa. Cikin ransa yana cewa, "in dai haka ne sarautar garin nan, Allah ya tsari gatari da saran dutse."
Daidai lokacin wani maroki ya tsaya gaban dokinsa ya daga hannu yana mai jinjina yana cewa, "Saraki sai Allah!"
Cikin fushi idanunsa a rufe, Matawalle ya ce, "ba wani Saraki sai Allah. Kurum ka ce Saraki sai Naira kanka tsaye!"

Comments
Post a Comment