Wata kotu a kasar Turkiyya ta daure Adnanu Oktar tsawon shekaru 1075 bisa laifin fasikanci da lalata da kananan yara da kuma halatta haram.
Adnan Oktar wanda ya shahara da rubuta littatafai da sunan Haruna Yahaya, mutum ne da ke da'awar kira ga addinin musulunci ta hanyar wasa da yada fasikanci da wulakanta masu adawa da shi. Mutum ne muzakkari wanda ya dauki komai halas komai muninsa indai zuciyarsa ta kaunaci abin. Wannan ta sa shi yake holewa da mata da yara kanana da dabbobi da sunan nishadi. Shi da kansa ya bayyana cewar shi fa mabukaci ne, bukata irin ta zuciyarsa ta fi ta waliyyai kuma karfin gabansa na iya hulda da mataye dubu!
Don haka ya gina wata katafariyar fada ba tare da sahalewar gwamnati ba. Ya radawa cibiyar tasa suna da 'Bilim Aras, tirma Vakfi' watau gidauniyar binciken kimiyya. A ciki ya zuba mata barkatai wadanda ya sa likitoci suka yi musu fiɗa suka zama masu kama iri ɗaya, wai su ne matan aljannar tasa. Yana kiransu, 'ya'yan maguna. Sannan ya tara ƙanana da ke karakaina suna yi masa hidima da kuma samari majiya karfi da yake kiransu Zakuna. Duk wadannan fa idan ya ga dama sai ya kirawo ya yi lalata da su ta yadda ya ga dama. Wata da ta kubuta daga tarkonsa ta je gaban kotu bayar da shaida, ta ce, sau tari idan ya bukaci dayansu, sai ya sa a kirawo wasu daga cikinsu suna kallo suna yi masa gurnani irin na maguna tare da ambaton wasu kalamai na shaukin masoya. Ta ce tun da take da shi ba ta taba jin ya ambaci Allah ba, amma ashar a bakinsa kamar zubar ruwan sama!
A zahiri kuwa, Adananu Oktar mutum ne zakakuri marubucin littattafan da suka kai kimanin 350 akan sha'anin mulki da rayuwa da siyasa. A farkon rubuce-rubucensa, an san shi da kafa hujjojin da ke dakile akidar Masoniya da kuma akidar Evolution ta Charles Darwin. Sai dai da tafiya ta yi nisa, sai ga shi tsundum cikin harkar Masoniya har ma ya bayyana cewar an ba shi wani babban mukami na matakin 33. Wani lokacin ma ya kan makala wannan lambar tasa a yayin da yake gudanar da wa'azinsa ta tashar talabijin dinsa.
An gano cewar duk littafan da yake wallafawa da sunan Haruna Yahaya ba shi ne ainihin marubucin ba, ya kan sayi rubutun da wasu suka yi, ko kuwa ya bayar da kwangila a yi rubutun da sunansa. Rubuce-rubucensa na farko farko sun fi jan hankali da komawa kacokam gare shi. Sai dai daga bisani sai ya koma zuga kansa tare da wata irin da'awar shi ne mahadi, shi ne wakilin Annabawa da sauran kalamai marasa kan gado.
Lokacin da aka kai samame gidansa an samu kwayoyin zubar da ciki da kwaroron roba kimanin guda dubu 69. Da aka tambaye shi abin da yake yi da su sai ya ce, ana amfani da su ne wajen gyaran fata. Masu nazari suka ce, ta yiwu yana tara maniyyin jama'a ne yana aikata wasu abubuwa da su.
Daga gidan talabijin dinsa ake watsa wa'azin da yake gudanarwa, wanda babu komai cikinsa daga molanka sai rawa da 'yan magunansa watau cikakkun 'yan matan da aka yi wa gyaran fata suka zama masu kama iri daya. Ya ce tun lokacin da yana yaro karami yake zuwa gidan rawa, anan ya ga irin wadannan matan, sai ya shiga bincike har ya gano yadda ake musu kwaskwarima su zama masu kama daya. Da ya samu damar hakan kuma ya shiga aiwatarwa kan mabiyansa.
Rigimamme ne kin ƙarawa, domin kuwa daga 2015 zuwa 2018 an ƙiyasta ya shigar da kara daban - daban har guda 5000. Duk wanda ya yi masa ba daidai ba, sai ya maka shi gaban kuliya. Daga bisani gwamnati ta gaji da tsiyatakunsa ta shiga bincike akansa.
A halin yanzu dai ta faru ta kare, an tabbatar da laifuka da dama akansa ta hanyar shaidu da ikrarin da yayi da bakinsa da kuma hujjoji bila adadin. Don haka nan take aka zartar masa da hukuncin daurin shekaru 1075 ba tare da zabin tara ba. Gidansa kuma, wanda ya gina ba da izni ba, ya shiga lalitar gwamnati.
To a Nijeriya ma kuma a Kano, muna da irin wannan takadiri wanda yanzu haka ya soma kawo da'awar mara kan gado tare da nuna farin cikinsa da aikin kafurai wanda a baya ya sha la'antarsu. Wannan mutumin ya soma tumbatsa har ya soma tunanin gina fada ta ƙashin kansa da zai rika gudanar da wa'azi da sauran ayyukansa. Bisa nazari da bincike, duk wanda ka ga yana aikata barna da sunan addini, da wuya ka raba shi da tu'ammali da miyagun kwayoyi da lalata da mata. Ko a Kano muna sane da labarin Mai Rakumi da yayi da'awar ana yi masa wahayin addu'a. Lokacin da mahukunta suka kai samame gidansa, sai ga tulin miyagun kwayoyi da kudin jabu.
Ba wai kangararrun suna fakewa karkashin addinin musulunci ne kadai ne suke ci da buguzum ba. Ko a cikin maluman kiristoci an samu Paul Schafer, wani hamshakin mai wa'azin Kirista na kasar Jamus da laifin tu'ammali da miyagun kwayoyi da kuma lalata da kananan yara. Duk wani shugaban addini da zai kawo rikita - rikita sabanin abin da aka saba da shi a hankalce da addinance da al'adance, ku bincike shi sosai. Yana fakewa ne da guzuma domin harbin karsana.
Idan gwamnati ta yi saken nata da ta saba, babu shakka nan gaba kadan Abduljabbar zai yi fito da wata fitinar da babu mai kashe ta sai ikon Allah.
Comments
Post a Comment