KARATU A INTANET


Sakamakon bullar cutar Korona, makatantu da dama suna ta kokarin hada karatunsu da intanet. Haka nan ana ta bude kamfanoni masu kwarewa kan haka. Ko a Nijeriya ma an bude wani sabon kamfani mai suna Roducate wanda ke samar da hanyoyin karatu a intanet tun daga aji daya na Firamare har zuwa ajin karshe na Jami'a.



RABE - RABEN KARATUN INTANET
Shi tsarin karatu a intanet ya kasu kashi-kashi. Bari mu duba wasu daga cikinsu.
A. Flipped course - Kayan karatu na bai daya wadanda ake kira open source masu lasisin Creative Common.

B. Hybrid course - Karatun da ake a aji amma ana dauka a bidiyo a ajiye saboda gaba. Jami'ar MIT da Harvard suna yin haka.

C. Face to Face: Tsarin karatun malami da dalibi ta intanet karkashin manhajojin sadarwa kamar Skype, Instagram, Zoom da sauransu. 

D. Web based: Karatu ta karkashin manhajojin intanet. Duka littafai ma anan za a same su.

E. Web enhanced: Karatun intanet amma ana aiko da littafi ko bidiyo a sauke a rika amfani da shi ko da ba a shiga intanet ba.

F. Mooc: Karatun dubunnan mutane a lokaci guda saboda karantar da su wani darasi na musamman. 

G. Audit Learning: Wasu wuraren suna bada damar ka yi karatu da su kyauta, amma babu satifiket har sai ka biya kudin jarrabawa. Jami'ar Harvard tana bada damar haka. 


DABARUN KOYO DA KOYARWA A INTANET

A karkashin wadannan rabe-rabe akwai dabarun da ake yi wajen koyo da koyarwa. Ga wasu daga cikin dabarun:
i. Synchronous Online Learning - Shi ne yanayin da malami da dalibai ke haduwa a lokaci guda su yi karatu. Malami yana daga can dakinsa tare da kwamfuta da kyamera da makirfo. Su ma dalibai haka. Ana ganin juna ana iya tambaya nan take a bada amsa. Ko a Nijeriya ma, Budaddiyar Jami'a, National Open University of Nigeria (NOUN) na aiwatar da wannan dabara tare da amfani da manhajoji irin su Zoom, Wiziq da sauransu. 


ii. Asynchronous Online Learning; shi kuma wannan ba lallai ne dalibai sai sin hadu a lokaci guda ba. Kowa zai iya shiga aji lokacin da ya ga dama, yayi tambaya ga malami idan ya so hakan. Malami na iya amsa tambaya a kebe ko a bayyane. Makarantun jami'a kamar Ahmadu Bello University sashin Distance Learning suna aiwatar da wannan tsari. Manhajojin da ake amfani da su sun hada da Moodle, Atutor, Ispring, Talent LMS da sauransu. 

iii. Fixed Learning - Shi ne dabarar koyar da karatu ta intanet bisa kayyadaden lokaci. Idan dalibi ya wuce lokacin bai yi rijista ba, to sai dai ya jira wani lokacin. Haka jarrabawa da sauransu. Irin wannan tsarin jami'o'i ke amfani da shi. Haka kuma wurare kamar su Future Learn, London School of Business suna aiki da wannan tsarin.

iv. Flexible Learning: Ana barin mutum yayi ta karatu son ransa, duk lokacin da ya ga dama ya shiga ko ya fita. Yawanci ba a jarrabawa a irin wadannan karatuttuka kuma ba a korar mutum sai dai mutum ya kori kansa. Ba a hanawa ba a gyarawa matukar ba hayaniya ka tayar ba. Ana amsa tambayoyi, yawanci malaman suna daukar kansu a matsayin abokan dalibai saboda babu bambanci tsakani. Dalibi a wannan aji yana iya zama malami a wani aji yayin da malamansa a wani ajin suke dalibansa a wani ajin. 
Wurare da dama kamar Udemy da Cousera da Udex da Khan University suna gudanar da irin wannan tsarin.

v. Adaptive Learning; Wannan tsarin ana shirya ne gwargwadon bukatun mutum. Kowanne dalibi zai zabi irin yadda yake so yayi karatunsa da irin darasin da yake son farawa da shi da kuma yadda zai zana jarrabawarsa. Tsarin yana bukatar lokaci a tsara komai daki daki kuma akwai kashe kudi ga dalibi. Dalibi yana iya zabar dakinsa a matsayin inda zai yi jarrrabawa, su kuma malamai daga sassan duniya sun zuba masa ido ta kwamfutocinsu suna kallonsa. 
Kamfanin Microsoft da ACCA da Oxford University suna aiwatar da shi. A kwanan nan kuma wasu jami'o'in kamar Harvard da MIT suna shirin shiga cikinsa. 

vi. Computer Aid Learning: Shi wannan dabarar dalibi zai shiga aji yayi ta karatu tare da taimakon kwamfuta cikin yanayin nishadi watau kamar game. Idan jarrabawa ta zo za a saka masa matakan tsaro na kwamfuta. Wuraren da ke aiki da haka sun hada da Shawn Academy da Duolingo da AIU da Smartly da sauransu.

vii.. Distance Learning: Shi ne tsohon tsari tun kafin zuwan intanet, inda dalibi ke karatu a gida ana aika masa da darussa ta gidan waya. Kayan koyon karatun sun hada da kaset da CD da Bidiyo da kuma littafai. Zuwan intanet ya kara bunkasa dabarar ta inda wuraren da ke aiwatar da shi suka zamanantar da shi. Sun hada da NOUN da University of Reading, UCLA, Writers Bureau da sauransu. 



A rubutu na gaba, zan zo da yadda ake yin rijista a wasu wuraren kamar Udemy (Inda na samo takardun nan) da Future Learn da Sylor da sauransu. 


Comments

Post a Comment