Akwai dubunnan wurare a intanet da ke bayar da horo da koyarwa ta yadda mai hali zai yi karatunsa kuma ya karbi takardar shaida. Ingancin karatun ko horon ya danganta da inda mutum ya yi. Yawanci masu bayar da horo sun fi amfani da tsarin MOOC (Massive Open Online Courses), amma daga ciki akwai masu bada horo har zuwa matakin digiri na biyu da kuma wani bangare na digiri na uku.
Yanzu bari mu duba wasu daga fitattun wuraren da ake iya samun takardun shaidar horo masu inganci:
Edx: Hadakar farfesoshi daga Jami'ar da Harvard da MIT a 2012 suka samar da wannan farfajiya domin bayar da ilmi kyauta da kuma saukakawa masu nwman kwarewa a fannonin ilmi. Suna samar da darussan da ake koyarwa a jami:oin ne tare da ɗaukar bidiyon malami a aji lokacin da yake wa dalibai lakca. Dalibai a Edx suna iya aikawa malamin tambaya ta hanyar email, shi kuma ya amsa idan yayi nazari.
Akwai dalibai kimanin miliyan 18 da ke karatu a wajen. Wasu daliban suna amfani da takardar shaidar da suka samu anan zuwa karatu na gaba.
Coursera: An bude shi a 2012 inda wasu farfesoshi ne daga Jami'ar Sitanfod da ke Amerika suka samar domin saukakawa dalibai yin nazari da karatu. An ƙiyasta dalibai kimanin miliyan 47 ke karatu yanzu haka. Kowa na iya zuwa yayi karatu ba tare da ya biya ko kwabo ba, amma babu malamin da zai kula da shi har sai ya biya wasu 'yan kudade a wasu kwasa-kwasan sannan a iya bashi aikin gida tare da jarrabawa. A karkashin farfajiyar akwai jami'oi kiman 50 da doriya da ke bayar da karatu. Ana iya karatu anan har zuwa digiri na biyu.
Future Learn: A cikin shekarar 2012 Jami'ar Open University ta Ingila hadi da wasu kamfanoni suka samar da farfajiyar domin bada horo ga masu son inganta turancinsu. Ya zuwa yanzu akwai kungiyoyin ilmi da jami'o'i kimanin 175 da ke mu'amala da su, kungiyar British Council na cikinsu.
Futurelearn na bayar da horo kan darussa masu yawa daga jami:oi da dama. Yawanci manyan farfesoshi da daktoci ne ke bayar da horo yayin da dalibai ke da ikon yin tambaya ta hanyar da aka tanada. Kowanne darasi akwai lokaci da ake gabatar da shi.
Ya zuwa yanzu akwai dalibai kimanin miliyan 11 daga sassa dabab daban na duniya.
Udemy: An bude Udemy a 2010 domin bayar da horo kan kwarewa kan wani aiki ko sana'a. Galibi farfajiyar ta fi bada himma wajen bayar da horo maimakon karatu irin na jami'a. Don haka ma babu tsayayyen malami ko dalibi anan. Kowanne mutum na iya zama malami a wani darasi kuma ya zama dalibi a wani darasin.
Idan mutum ya maida hankali a Udemy zai koyi abubuwa da dama na kwarewa wadanda ba a koyar da su a jami'a. Kusan kowanne irin abu na kimiyya da fasaha da zamantakewa da tattalin arziki ana samun darasin da ake koyarwa anan. Duk darasin da mutum ya kammala zuwa 100% za a aika masa da takardar shaida.
Ya zuwa watan Janairu, 2020 an ƙiyasta akwai masu daukar darasi kimanin miliyan 53 da malamai dubu 57 da darussa sama da dubu 150. Ana koyar da darussa cikin harsuna kimanin 65.
Sai dai Udemy bashi da amincewar wata hukuma watau 'accreditation' kasancewar malamai masu koyarwar sun fi mai da hankali wajen samun riba da jawo hankalin mutane su yi ta sayen darussa suna koyi da kanka.
Akwai tsarin tambaya da amsa da kuma neman karin bayani ga mai gabatar da darasi. Kana iya nuna rashin gamsuwar ka ga yadda mai gabatar da darasin ke yi. Idan baka gamsu ba, sai ka yi tawaye ka amshi kudinka.
Akwai darussa na kyauta da kuma na garabasa da malaman ke bari a shiga kyauta daga lokaci zuwa lokaci.
Bari mu tsaya haka duk da akwai dumbin wurare kamar Udacity, Shaw Academy, Khan University, Saylor, Skillfeed, Oracle University, Laracast, da Lynda.
Rubutu na gaba zai zo ba da jimawa ba.
Comments
Post a Comment