HARAJIN NAWA ZA KA BIYA?
Ya kamata kowanne dan kasa nagari ya sani cewar biyan haraji ga gwamnati wajibi ne. Kamar yadda aka ambaci hakkin dan adam a cikin dokar kasa, haka aka ambaci biyan haraji a cikin ta. Don haka dan kasa nagari shi ne mai biyan haraji daidai gwargwado.
Inda gizo ke sakar shi ne ta wajen gane ainihin abin da mutum zai biya duk shekara gwargwadon kudin da ya samu a cikin shekarar gaba daya. Hanyoyi uku ake lissafa haraji. Hanya ta farko shi ne ta daidaikun mutane, ana lissafa abin da mutum ya samu a shekara. Ma'aikaci ana lissafa albashin da aka biya shi. Dan kasuwa ana lissafa cinikin da yayi ko ribar da ya samu a cinikin shekara. Gwamnatin jihar da aka samu kudin ce ke da alhakin karbar harajin.
Hanya ta biyu kuma shi ne lissafin harajin kamfanoni masu zaman kansu. Ana lissafa cinikin da suka yi da hannun jarinsu da kuma irin ribar da suka samu da sauransu. Gwamnatin tarayya ce ke karbar wannna harajin.
Hanya ta uku kuma shi ne lissafin harajin kamfanoni masu hakar danyen man fetur da gas da abin da ya dangance su. Ana lissafa adadin gangar man da suka zuko da irin ingancinsa da kuma yawan iskar gas da suka kona da sauran abubuwa. Wannan ma gwamnatin tarayya ce kadai ke karbar sa.
A yau zan yi bayani ne akan lissafin harajin daidaikun mutane da maaikata wanda ake kira Personal Income Tax (PIT).
Ma'aikacin gwamnati shi ya fi kowa biyan haraji, saboda shi ana yankewa ne tun daga tushe gwargwadon abinda ya samu a wata, wanda ake kira Pay As You Earn (PAYE).
Yadda ake lissafin shi ne, da farko za a kiyasta abin da zai iya samu a shekara bisa matakin albashin da yake kai. Abin da aka samu sai a kara 5% na kiyasin kudin kayan more rayuwa da aka ba shi. Watau kamar an bashi motar ofis da direba ko gida.
A lissafin da aka samu a cire dubu 200 a matsayin alawus, amma idan mutum yana samun sama da miliyan 20 a shekara za a cire 1% ne a matsayin alawus. Wannan shi ake kira 'Consolidated Relief Allowance (CRA). A baya ana cire alawus ne daga yawan iyalin mutum da kuma nau'in aikinsa. Yanzu kuwa an hade shi gaba daya babu bambanci.
Daga haka sai a cire kudin da ake diba daga albashin mutum na fansho da na gidaje da kuma na inshorar lafiya. Idan mutum yana biyan wata inshorar kamar 'life insurance' nan ma za a cire kudinta. Haka nan za a cire kudin fansho na kashin kai da mutum yake zubawa.
Idan dan kasuwa ne ana cire kudin ruwa da ya ciyo na bashi da kuma kudin bashin da aka cinye masa da kudin da ya samu daga ribar kamfani da sauransu.
Daga abin da ya rage ne ake iya lissafin kudin da zai biya na haraji. Ana karkasa kudaden ne zuwa rukuni - rukuni kamar haka:
*** Dubu 300 din farko za a cire dubu 21,
*** Dubu 300 ta gaba za a cire dubu 33,
*** Dubu 500 ta gaba za a cire dubu 75,
*** Dubu 500 ta gaba za a cire dubu 95
*** Miliyan 1 da dubu 600 ta gaba za a cire dubu 336,
**** Abinda ya ragu daga miliyan 3 da dubu 200 za a cire 24%.
Idan aka tattara gaba daya na kudaden da aka cire a wadancan rukunoni sai a raba 12. Wannan ne ainihin abin da mutum zai rika biya a duk wata.
Ma'aikacin da yake daukar daukar albashin dubu 30, za a rika cire harajin da bai wuce naira 514 ba duk wata. Wanda ke samun dubu 100 kuwa, ana yanke masa naira 6 da dari 5 (6,500). Kenan wannan tsarin yana tausaya mai karamin samu akan mai samu da yawa. Ana kiran tsarin da 'Progressive Tax System'.
Ga waÉ—anda yake da wahala a iya gane adadin kudin da suke samu duk shekara, doka ta bayar da iznin a kiyasta harajin da za su biya bisa la'akari da wasu ka'idoji. Wannan ake kira 'Best Of Judgement'. Amma idan mutum bai yarda da kiyasin ba yana iya yin korafi. Idan ba a gyara ba, zai iya kai hukumar tara harajin kara a kotun musamman da aka tanada domin al'amuran haraji.
Da fatan jama'a kowa zai lissafa samunsa ya ruga hukumar tattara haraji ya sauke nauyin da ke kansa.
Akwai amfani mai yawa kan haka. Rubutu na gaba zai zo da wasu daga amfanin biyan haraji ga dan kasa nagari.

Comments
Post a Comment