YADDA AKE RARRABA KUDADE TSAKANIN GWAMNATIN TARAYYA DA JIHOHI

KU ZO KU JI - 1


Da farko dai akwai bukatar mu san cewa, asusun gwamnatin tarayya iri uku ne; na farko ana kiransa Consolidated Account, anan ne gwamnati ke kashe kudaden da ta samu. Na biyu sunansa Federation Account, shi ne wanda ake rarraba abin da ke ciki tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi da kananan hukumomi. Na uku ana kiransa Development Account, ba a taba shi sai akwai bukatar aikin gina kasa ko yaki da lalacewar kasa.


Zan yi magana akan asusu na biyu watau Federation Account. Duk kudin da aka samu a kasar nan yana shiga ne cikin wannan asusun in ban da harajin jami'an tsaro da na mutanen da ke zaune a birnin Abuja. Wadannan suna shiga Consolidated Account ne kai tsaye.

Idan an tattara kudaden duka, sai a kwashi 13% a mikawa jihohi masu arzikin ma'adinai. Hukumar NNPC ana ba ta ladan 7%. Hukumar Kwastam da FIRS da sauran hukumomin da ke samar da kudaden shiga ana rarraba  4%  gwargwadon bajintar da suka nuna wajen tara kudin.

Idan an yi wannan kasafin, abin da ya rage sai a dankawa gwamnatin tarayya 52.68%. Jihohin Nijeriya kuma guda 36 a raba musu 26.72%. Abin da ya rage na kashi 20.6% kuma sai a rarrabawa kananan hukumomi su 774.
Daga cikin abin da gwamnatin tarayya ta samu, tana mikawa birnin tarayya 1%, Development Account 3%, matsalolin zaizayar kasa 2% sauran kuma da su ake gudanar da ayyukan yau da kullum na albashi da sauransu.

Kudaden da aka samu wanda za a rarrabawa jihohi kuma ana karkashi kamar haka:

👉40% ana raba shi daidai wa daida ga kowacce jiha.

👉 30% Gwargwadon yawan jama'a

👉 10% Gwargwadon fadin kasa da yawan duwatsu

👉 10% Gwargwadon kokarin jiha na tara harajin cikin gida

👉 10% Gwargwadon irin aikin da gwamnatin jiha ta gudanar a jihar kamar a bangaren ilmi 4%, lafiya 3% da ruwa 3%. A wajen lafiya ana lissafi har da yawan gadajen asibiti da jihar ke da su.

Kasafin kananan hukumomi kuwa, ana rarraba musu ne tare da karin 10% na gudunmawa daga abin da jiharsu ta tara sannan a karkasa shi tsakaninsu kamar haka:

👉 Raba dai-dai
👉 Yawan jama'a
👉 Fadin kasa
👉 Yawan makarantun firamare
👉 Hobbasa wajen samun kudin shiga, da sauransu.

Wannan tsarin hukumar RMAFC ce ke da alhakin aiwatarwa tare da gudunmawa daga wasu kwamitocin gwamnatin tarayya da na jihohi da ake kira, Federation Accounts Allocatioj Committee (FAAC) da kuma State Joint Local Government Account Allocation Committee (SJLGAAC)


- Danladi Haruna
10th July, 2019

Comments