WANDA ZAI BA KA RIGA... 3

WANDA ZAI BA KA RIGA... 3
.

Shi dai Sergey Panteleevich Mavrodi,  ana yi masa lakabi 'Pied Piper Of Hamelin'  watau kwatankwacin Sarkin Busa wanda labarinsa ya bayyana a littafin Magana Jari Ce. Dalili kuwa,  mutum ne da ya shahara wajen fuska biyu; ta karya da ta gaskiya. Kai tsaye yake shaida wa mabiyansa cewar akwai hadari fa cikin abin da yake aikatawa amma a gefe daya kuma yana shaida musu cewar tsarinsa shi ne ingantaccen gwadabe da za a iya rabuwa da talauci har abada.
.
A shekarar 1989 Sergey Mavrodi da kaninsa,  Vyacheslav Mavrodi da kuma wani mai suna Olga Melnikova suka bude kamfani da sunayensu na biyu watau MMM. Suka soma safarar kwamfutoci daga kasar Amerika zuwa Rasha. Babu jimawa kamfani ya durkushe saboda an kama su da laifin kin biyan kudin haraji. Bayan haka cikin 1993 suka shiga hada - hadar kudi inda suke karbar hannun jari daga jama'a tare da alkawarin biyansu da ribar kashi 1000 watau ninki goma na abin da mutum ya zuba. A lokacin kuwa Rasha ana fama da matsin tattalin arziki, farashin kayayyaki kullum yana ara hauhawa.
.
Mutane da suka ga hanyar samun kudi asiri rufe,  sai suka yi ta sayar da kadarorinsu suna ta zubawa. Kamfani kuma kullum yana fada a kafafen rediyo da talabijin cewa sun samu riba niniki dubu 10 ko dubu 20, suna da hannun jari miliyan dubu kaza. Sai daga bisani lissafin kudin ya gagara,  sai dai su ce suna da hannun jari cikin daki kaza na kudin kasar Rasha watau Robul.  Da lissafin ya wuce hankali,  sai shugaban kasar Rasha na wancan lokacin,  Boris Yelsin ya fitar da dokar da ta hana kamfanin MMM ya bayyana adadin hannun jarinsa a bainar jama'a.
.
Ganin kamfanin MMM ya samu nasara,  sai wasu kamfanoni irinsa suka bayyana,  kowanne ya dage da talla da romon baka. Wani daga kamfanonin ma ya yi alkawarin zai biya ribar ninki dubu 30 na abin da mutum ya zuba bayan shekara daya.  Ganin haka ya sa Mavrodi da tawagarsa suka bullo da dabarun jan hankalin masu zuba hannun jari zuwa gare su. Suka fito da tsarin daukar mutane kyauta a motocin haya,  da biyan kudin asibiti ga marasa lafiya da sauran dabarun musamman a kauyuka inda babu masu dogon bincike dangane da abin da me wakana a gari.
.
A watan Yuli 1994 'yansanda suka rufe ofishin MMM bisa zargin ya ki biyan kudin haraji daidai.  Da ma mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Duk da an bude ofishin bayan wasu kwanaki,  sai Mavrodi ya sanar da cewa gwamnati ta kwace masa hannun jari,  don haka sun durkushe. Ya dora laifo kacokam ga gwamnati. Wannna ta sa aka samu mutane fiye da 50 sun kashe kansu saboda bakin cikin abin da suka yi asara kusan dala miliyan 5.
Duk da haka,  mutane suka fito zanga zanga suna goyon bayansa tare da kiran gwamnati da ta saki kadarorin kamfanin MMM da ta kwace. Da yake munafukin ya san irin abin da ya kulla,  Mavrodi ya ki yarda a sasanta da gwamnati,  kullum yana zarginta kan kassara masa kamfani.  Daga bisani aka bayar da umarnin a kamo shi,  sai ya yi wuf ya shiga siyasa.
.
Tare da amfani da masu hannun jarin da ya yaudara,  ya yi ta kamfe cewa zai fito takarar shugaban kasa. Bayan an jima ana ja - in - ja,  gwamnati ta janye umarnin kama shi,  shi kuma ya janye aniyar takarar shugaban kasa,  to amma ya fito takarar dan majalisa daga jihar Duma. Wannan ta sa ya samu rigar kariya daga tuhumomin da ake masa.  Sai dai kuma a shekarar 1996 aka janye rigar kariyar da yake da ita a matsayinsa na mataimakin kakakin majalisar jihar Duma.  Saboda haka ya shiga wasan buya bayan ya ayyana kamfanin MMM da cewa ya durkushe.
.
An ce daga nan ya gudu Amerika ya bude wani kamfani mai suna Security Generation wanda ke biyan kashi 200 na riba ga masu hannun jari. Wasu kuma suka ce bai tafi ko'ina ba,  ya buya ne a birnin Moscow yana biyan wasu karti suna gadinsa tare da kawo masa tsegumin abubuwan da ke faruwa a kasa. Babu jimawa kamfanin SG ya durkushe bayan ya waske miliyoyin dalolin mutane.
.
A shekarar 2003 aka gano inda Mavrodi yake aka cafke shi. Aka ba shi kwafin korafe - korafen da ake akansa,  littafi 650 kowanne na kunshe da shafuka 300. Aka ba shi shekara 3 ya kammala karantawa tare da nazari da kare kansa.  Bayan shekara 3 aka same shi da laifi,  aka daure shi tsawon shekara hudu da rabi. To amma da yake ya jima a daure a kurkuku,  bai fi wata guda ba aka sake shi.
.
Da ya samu kansa sai ya sake tunani inda a shekarar 2008 ya fitar da wani littafi mai suna 'Temptation' aka wallafa guda dubu 7. A ciki ya bayar da tarihin gwagwarmayar sa da irin kudurinsa na kawo karshen hanyoyin hada hadar kudi ta yadda wai kowa zai zama hamshakin mai kudi.  Wannan ta sa gwamnati ta sake cafke shi aka daure shi shekara biyu.  Bayan ya fito sai ya kirkiro da wani sabon kasuwancin da ya radawa suna MMM - 2011. A bisa tsarin wannan kasuwanci,  babu wani asusun da ake ajiye kudi a banki,  kudaden za su rika musaya ne tsakanin jama'ar da suka rungumi tsarin.  Ya radawa kudin da ake ta'ammali da su a wannan tsarin suna Mavro.  Idan ka zuba dala 100, to sai a ce kana da Mavro 100 kuma bayan wata daya za su koma Mavro 130. Ya ce nufinsa shi ne samar da hanyoyin azurta kai ba tare da wahala ba.
.
Duk da shirin ana yinsa a kasar Rasha,  amma jama'a na kaffa - kaffa da shi. Don haka ya fantsama duniya tare da 'yan kanzaginsa. Ya kafa reshe a Indiya da Thailand da Afrika ta Kudu da Zimbabwe. A farkon shekarar 2016 ya shigo Nijeriya da kafar dama. Domin kuwa an ce yanzu haka mutane sun zuba hannun jari sama da dala miliyan dari da hamsin kuma akwai membobi kusan miliyan daya da rabi,  kullum kuma karuwa suke yi.
.
Abin mamakin shi ne,  yawanci masu zuba hannun jarin sun san irin kasadar da suka afka,  domin ko a gidan intanet na MMM Nigeria an yi gargadin cewa a yi hattara domin akwai gangaci kuma ba banki ba ne ko matattarar kudi. Da yake jama'a idanunsu sun rufe da son abin duniya da hadama,  basu damu ba,  duk da cewa hukumar hada -  hadar kudade ta kasa (SEC) tana gargadi dangane da MMM amma kullum samun al'umma masu shiga ake yi.
.
Yadda suke yi shi ne,  za ka zuba kudinka a bankinsu, idan sun shiga za a ba ka Mavro na adadin kudinka. Sai ka yi nufin bayar da gudunmawa, za a nuno maka wanda za ka ba shi gudunmawar. Duk abin da ka ba shi sai ka jira sai bayan kwanaki 30 sai kai ma ka nemi gudunmawa.  A lokacin kuwa abin da ka bayar ya karu da kashi 30. Sai a nuna maka wani can daban da zai ba ka gudunmawar. Wannan ta sa kila gwamnati ba ta dauki mataki ba,  saboda tsarin da suke bi ta wajen bayar da gudunmawa.
.
Masana na hasashen wannan tsarin da wahala ya dore zuwa watanni ukun farko na shekarar 2017. Wasu kuma suna ganin cewa tsarin zai karye ne ta fuskoki uku; fuska ta daya,  idan aka rasa wanda zai zuba hannun jari. Fuska ta biyu idan duk masu hannun jari sun nemi gudunmawa a lokaci guda,  fuska ta uku kuma idan gwamnati ta fito da wasu dokoki domin kawo karshen wannna irin harbati matin kasuwanci. Wannan hasashe dai ya tabbata, domin kuwa a cikin watam Disamba na 2016 rana tsaka MMM suka rufe bada kudi gudun wadanda za su dauka domin tanadin kirsimeti. Daga wannan lokacin kuwa har zuwa yau kullum sai an samu wadanda suka tafka asara ta miliyoyin nairori karkashin shirin.
.
Kodayake akwai kasuwanci na halali da ake kira Network Marketing wanda ya so ya yi kama da Pyramid Scheme.  A rubutu na gaba zan zo da bambancin da ke tsakanin Network Marketing da Pyramid Scheme da yadda za a gane na gaskiya da na karya a cikin su.

Comments