FADI TASHIN SARAKUNAN KANO KARKASHIN MASU MULKI
.
Sannu a hankali darajar sarakunan musulunci, jikoki da tattaba kunnen askarawan da suka karbi tutoci daga hannun Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo ta rika faduwa tun bayan da turawan mulkin mallaka suka ci garuruwansu da karfi tuwo.
.
Kano ma ba ta tsira daga faduwar darajar sarauta ba. A cikin watan Fabarairu na 1903 mayakan turawa suka shiga cikin birnin Kano bayan sun kashe dubunnan mutane, su kuwa ba dududu mutum 14 ne kadai suka samu 'yan raunuka, biyu daga ciki ne kadai turawa, ragowar duk bayinsu ne suka raunata.
.
Duk da sun shiga birnin ta karfi ba su iske Sarkin Kano a cikin gari ba, ya tafi Sokoto wajen mai martaba Sarkin Musulmi Attahiru II. Saboda haka suka aika runduna cikin hanzari domin a kama sh. An tarar da rundunar Sarkin Kano Alu kuma aka shata daga. Anan ne ma wani danuwansa kuma wazirinsa Ahmadu ya yi Shahada.
.
Bayan Sarki ya zo hannu, sai suka tafi da shi zuwa Adamawa, daga bisani aka canza masa mazauni zuwa Lokoja inda ya rasu a can. Alu Babba shi ne na farko a sarautar Kano da ya gamu da wulakancin masu mulki duk da irin tsananin fushinsa da karfinsa da juriya da kuma dumbin ilmin da Allah ya hore masa.
.
Bayan tumbuke Sarki Alu sai Turawan Mulkin Mallaka na Ingilishi sun kafa tsarin mulki na mulki ta hannun yan kasa (Indirect Rule) a arewacin Nijeriya saboda kasancewar suna da masarauta da take da tsarin mulki na bai daya (Centralized Political System) wannan ta sa suke gudanar da mulki ta hannun sarakuna.
.
An danka rikon garin Kano a hannun Abbas Makerim doki jikan Dabo. Bayan wata uku watau cikin Mayu na 1903 aka tabbatar masa da sarautar Kano, sai sai dai cike da wasu sharudda masu sarkakiya da walagigi da sarauta. Wani tsohon bature mai suna E. D Morel ya bayyana irin fadi tashin da ya sha ga Sarki Abbas wajen samun amincewarsa turawan mishan su kafa makarantu da coci a fadin Kano. Cikin 1919, Sarki Abbas ya rasu.
.
Bayan mutuwar Abbas, sai aka nada Sarki Usman na biyu wanda ya gamu sa tarnaki daga turawan mulki wajen hana shi tafiyar da mulki yadda ya kamata ga kuma tsufa da ya cim masa.
.
A watan Afrilu na 1926 Sarki Usman II ya koma ga Mahalliccinsa. Sarauta ta koma ga Abdullahi Bayero amma ba a amince masa ya nada manyan bayi da ke taimakawa sarki ba. Wadannan bayi sun hada da Shamaki, Shantali da Sallama da kuma Danrimi. Wannan ta sa Sarki Abdullahi Bayero ke cewa, "an bamu riga mu sa, amma an hana mu fitar da hannayenta."
.
Duk da kokarin wannan basarake an ce turawa sun hana shi motsawa yadda ya kamata wajen matsa masa ya yi nadi ko ya cire rawani daidai yadda suke bukata karkashin tsarin nan na Indirect Rule.
A karshen rayuwarsa ne aka samu bullar jam'iyyun siyasa inda wasu matasa da suka hada da Abba Maikwaru, da Bello Ijumu da Babaliya Manaja da Musa Kaula da Abdulkadir Danjaji da Musa Bida da Magaji Dambatta da kuma Mudi Spikin suka dauki gabarar samar da jam'iyyar NEPU wadda kai tsaye take adawa da manufofin turawan mulkin mallaka tare da kalubalantar ba tare da tsoro ba.
.
Duk lokacin da aka kama dan Nepu sai a gurfanar da shi gaban Sarki bisa hujjar cewa sun kafirta domin suna aibata shugabanni suna zaginsu. Don haka a kashe su. Sarki Abdullahi Bayero bai taba yarda da wannan ikrari ba, yana mai cewa, "tabbas akwai wani zunubi da muka aikata, don haka Allah ya jarrabe mu da samuwar wadannan yara."
.
Wannan kuduri na Sarki bai yi wa da yawan masu mulki dadi ba. To amma yaya za su yi da shi?

Comments
Post a Comment