WANDA ZAI BA KA RIGA... 1

WANDA ZAI BA KA RIGA... 1

Watakila saboda halin matsin tattalin arzikin da ake ciki a Nijeriya ya sa jama'a kowa ya shiga fafutukar hanyoyin da zai samu rangwamen wahalhalun da ake ciki. Hanyoyin kuwa sun hada da masu kyau da marasa kyau, masu sauki da masu wahala, masu bullewa da marasa bullewa.

An samu bayyanar wasu mutane da ke amfani da wannan damar wajen nunawa jama'a cewar wai za su samar musu da saukin rayuwa ta hanyar biyansu kudade masu yawa idan sun zuba hannun jari. Wasu na cewa duk abin da ka zuba a kamfanin, bayan wasu kwanaki za a ba ka ninkinsa. Wannan shi ake kira 'Ponzi Scheme', kuma ana masa kirari da 'Rob Peter to Pay Paul'.
Wasu kuma suna cewa idan ka zuba kudi, kuma za ka nemo wasu mutanen su zuba jari karkashinka, duk abin da suka zuba kana da wani kaso na musamman a ciki. Irin wannan ana kiransa 'Pyramid Scheme' ko 'Multi Level Marketing' . Dukkan wadannan hanyoyi ana iya kawo wani abu da sunan shi ake sayarwa musamman duwatsu masu daraja kamar Gwal, ko Azurfa, ko Deman da sauransu. Ana iya sayar da wasu abubuwan ma da ba su kai kimar wadanda na ambata ba kamar magunguna da kayan adon gida. Ana iya samun masu sayar da kaya nagari amma da yawansu sun fi mayar da hankali wajen samun sabbin membobi maimakon abin da suke sayarwa.

Wannan kasuwanci ne mai hadarin gaske, karewar ta ma ba a taba samun mutumin da ya wanye lafiya a cikin harkar ba. An sha samun bullar macutan mutane a kasashe da dama tare da irin wannan kasuwanci amma a karshe sai an yi rabuwar dutse a hannun babbar riga.

Kodayake, an sha samun bullowar irin wannan al'amari a Nijeriya, to amma yanzu kasancewar akwai saurin yaduwar bayanai ta kafar intanet, sai ya zamana an same su da yawan gaske suna shiga lungu da sako suna cutar bayin Allah da romon baka wanda hankali ba zai taba dauka ba.

A binciken da na yi, daga watan Janairu na wannan shekara ta 2016, zuwa watan Satumba, an samu bayyanar irin wadannan kamfanoni sama da guda saba'in wadanda ke amfani da kafafen sadarwa na zamani suna damfarar mutane da suna kasuwancin zamani mai riba. A jumlace, wadannan kamfanoni suna da masu hannun jari fiye da miliyan ashirin (bisa kiyasi ), sun karbi kudin mutane sama dala miliyan dari biyu.

Manya daga wadannan kamfanoni akwai wanda ake Mavrodi Mondial Movement (MMM) da Enisplus da Oriflame da Tianshi da GNLD da Forever Living da HappyLife da sauransu. A cikin wadannan kamfanoni akwai masu sayar da kayayyaki da magunguna amma irin sharudan da suke gindayawa za ka fahimci akwai ayar tambaya dangane da irin romon bakan da suke lasawa mutane.

A rubutu na gaba, zan yi magana game da ma'anar Ponzi Scheme da Multi Level Marketing sannan kuma zan kawo wani abu daga shahararrun barayin da suka ci karensu babu babbaka a irin wannan kasuwanci tare da bayanin wasu daga kamfanonin da ke baje kolinsu yanzu haka a Nijeriya. Fatana dai, jama'a su hankalta su gane cewa duk wanda ya ce zai ba ka riga, to ka soma duba ta wuyansa.

Comments