NA ZAMA IMAMIYA

Da Allah ya sa na karanta wannan littafi mai taken Adabin Abubakar Imam wanda Farfesa Ibrahim Malumfashi ya wallafa shi a shekarar 2009, da kuwa littafina mai suna Tekun Labarai na daya zai kasance mai fasali fiye da yadda na wallafa shi.
Hakika wannan binciken kwakwaf da aka yi dangane da irin zurfin ilmi da tsananin bincike ds juriya da hazaka ta marigayi Abubakar Imam da yadda ya gudanar da rayuwarsa ta rubuce - rubucen adabi ya sake karfafa mini gwiwa yadda zan gudanar da nawa rubuce - rubucen da kuma yadda zan nemi albarkacin magabata da malamanmu. Wannan littafi ya zama tamkar wukar gindi da ke nuna cewa marubuci ba raggo ba ne, ya zama tilas ya tashi ya yi bincike kuma ya yi karatu tare da nazarin al'ummar da yake ciki dokin ya samar da ingantaccen rubutu wanda ko bayan ya kaura dag duniyar za a ci gaba da tunawa da shi ana yaba kokarin da ya yi. Saura kuma, Allah ya jikan magabata kuma ya sakawa malamanmu da alheri musamman bijimin malami, Ibrahim Malumfashi wanda ya gudanar da muhimmin bincike kusan shekaru 20 kafin haka ya cimma ruwa.


Abin da ya burge ni dangane da littafin Adabin Abubakar Imam shi ne, yadda aka yi bayani dalla - dalla dangane da tsittsigen kowanne labarin da aka bayar a jerin littattafan Magana Jari Ce da kuma dabarun da aka bi wajen hausantar da su har su zama tamkar asalinsu can hausa ne. Daga wannan na nakalci wasu dabarun masu dumbin yawa, wadanda nake fatan yin amfani da su a Tekun Labarai na 3.

Abin da za mu duba shi ne, wancan lokacin littattafai na matukar wahala da karanci ta yadda samunsu da karanta su da nazarinsu ke da matukar wahala. Sai jajirtacce, mai azama kuma mai zurfin ilmi kadai ke iyawa. To amma a yanzu da yake magabata sun riga sun sayar da ransu domin inganta rubuce-rubuce, babu abin da ya rage mana sai bin sawu irin nasu tare da fatan samun dacewa albarkacin kokarinsu. Irin wannan bajintakar magabata wacce da wuya a same ta a halin yanzu, abin da ya yi saura kurum shi ne yin azama daidai gwargwadon abin da ya samu.
Ga marubucin da ke bukatar yin ingantaccen rubutu, ya zama wajibi ya yi karatu tare da nakaltar hanyar da yake ganin ita ce mafi dacewa. Ni dai na rungumi IMAMIYA. Wani marubucin wannan zamani, Jeff Goins yana cewa, "kyautuwa ya yi idan za ka yi rubutu, ka soma nazarin ayyukan da suka gabata ta hanyar nazari, da bincike, da karatu. Ta haka za ka iya fahimtar daga ina aka taho, ina aka tsaya kuma ina za a nufa. Ta haka za ka iya samar da ci gaba gwargwadon yadda kake hasashe ko fiye da haka... "
Kira na ga dalibai da manazarta, kowa ya yi kokarin mallakar wannan littafi na ADABIN ABUBAKAR IMAM wanda IBRAHIM MALUMFASHI ya wallafa. Karanta wannan littafi kadai zai warware wasu takaddamomi masu yawa da na ga ana yawan tattauna su daga lokaci zuwa lokaci.

Comments