SATAR FASAHA?

SATAR FASAHA?
.
Wasu daga masu ganin kurilla sun gano wasu kalmomi cikin kalaman shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da aka aro daga kalaman da shugaba Barrack Obama ya yi a Amirka a 2008. A cikin jawabin na PMB wajen kaddamar da shirin 'Change Begins With Me' masu rubutun jawabin, sun makala wasu kalamai na bukatar sake jajircewa da kokarin da shugabannin suke yi na wajen gyaran halin da kasar nan ke ciki.
.
Yayin da aka gano haka, nan da nan gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki inda aka dakatar da wani babban jami'i, kuma aka ce a gabatar da bincike domin zakulo wadanda ke da hannu a wannan satar fasaha. Tuni kuma gwamnatin ta nemi afuwar Obama tare da bukatar 'yan Nijeriya su kalli sakon da ke ciki ba tare da wata manufa ta daban ba.
.
Koda yake, daga yadda aka zakulo wannan abu ya zama abin kunya da rashin iya tsari musamman ga ma'aikatan da ke kula da wannan rubutun. Ya dace mu fahimci cewar ba shugaban kasa ne ke da alhakin wannan al'amari ba. Kowanne shugaba yana da masu rubutu na musamman da suke bincike tare da tattara bayanai da tsara masa duk abin da zai fada kan manufar da gwamnatinsa ke kai da abin da take son cimma buri. Ke nan wadannan jami'ai ne suka yi azarbabi suka ara suka yafa musamman ganin irin hadafin da gwamnatin ke son cimma wa wanda ta yi wa lakabin 'canji'.
.
Babban kuskuren wannan rubutu kamar yadda aka yi ta yayatawa shi ne, rashin jingina maganar daga ainihin wanda ya soma yin ta watau Barrack Obama. Maimakon haka ma sai aka yi wa kalaman kwaskwarima inda aka kakkara wasu kalmomi da nufin canjawa daga ainihin jawabin.
.
Anan ina yaba wa shugaban kasa da gwamnati yadda aka yi hanzarin amsar kuskure tare da daukar mataki. Bai kamata a kyale duk wanda ke hannu wajen kunyata shugaban kasa haka ba. Haka kuma na yaba da yadda aka nemi afuwa da hanzari tare da bukatar a maida hankali ga sakon da ake son isarwa.
.
Kwafin kalaman wani da halin hankaka mai da dan wani naki ba farau ba ne a tarihin shugabannin duniya. Shi kansa Barrack Obama an yi zargin ya kwaikwayi kalaman da gwamnan Massach a 2006 shi kuma ya maimaita irin su a 2008 ba tare da ambaton inda ya aro ba. Wannan ta sa jama'a suka yi ta masa surutai har sai da ya nemi afuwa kamar yadda Buhari ya yi a yanzu.
Haka kuma yawancin kalaman da Melinia Trump, matar dan takarar shugabancin Amirka a jam'iyyar Republican tana kwaikwayon matar Barrack Obama ne ta fuskar furucin kalma bayan kalma. Shi kansa Donald Trump din ana cewa yana satar fasahar kalmomi ne daga Senator Joe Biden. Ko anan Afrika an sha samun kalaman Tanzaniya, John Magufuli na kwafo irin kalaman Kenneth Kawunda, tsohon shugaban kasar Zambia.
.
Ina ganin duk wadannan ba su zama laifi ba matukar burin da ake so wajen isar da sakon ya isa kuma an fahimci abin da ake bukatar cimma. Sai dai ya kamata a rika ambaton tushe da makama domin magance gutsuri tsoma.

Comments