YADDA AKE SAMUN BASHIN NOMAN SHINKAFA
Gwamnatin tarayya ta yi shiri na musamman domin bayar da bashi mai rangwamen kudin ruwa ga manoma. Wannan shirin da ake kira a turance, 'Anchor Borrower's Programme (ABP) an ware kimanin naira biliyan 20 da za a rarrabawa kananan manoman da za su yi noman shinkafa wanda zai inganta yadda ake nomawa da sarrafa shinkafa a kasar nan. A bisa tsarin dai za a ba wa manomin da ke noma eka daya bashin naira 208,080. Watau kimanin manoma dubu d'ari ne ke iya cin gajiyar shirin a tashin farko. Babban bankin tarayya, ya bayyana cewa za a iya kara yawan adadin kudin har su zama zuwa biliyan 220 ta yadda manoma sama da miliyan 10 za su samu tallafin a karon farko. Idan hakan ta faru za a iya samun adadin shinkafa metrik tan dubu 10, a yanzu dai an ce ana cin shinkafa kimanin metrik tan dubu 10. Wannan na nuna cewar idan shirin ya tabbata, kasar nan za ta iya fitar da irin shinkafar da take nomawa zuwa kasashen waje.
Sai dai da dukkan alamu har yanzu manoma ba su fahimci shirin nan sosai ba, a tsammaninsu yadda aka saba a baya ne, watau a karbo kudin a sha shagali da su. Daya daga abubuwan da ake bukata shi ne, wajibi ne mai neman bashin ya mallaki gona akalla kadada (eka) daya wadda zai noma shinkafa. Wajibi ya mallaki lambar banki ta BVN, sannan sai an samu kamfani ko hukumar da za ta tsaya masa. Haka kuma manomi ba zai samu bashi fiye da sau daya a lokaci daya ba. Duk da haka manoma na da wani hanzari ko dabarar da za su samu bashin fiye da daya.
A wajen tantancewa, ana samun manomi daya ya bayar da sunansa fiye da sau daya a wurare daban - daban. Ana samun mutum daya ya yi amfani da BVN da yawa, wani kuma sai ya sa sunansa da na matansa da na 'ya'yansa. Wani kuma ba manomin gaske ba ne, kurum ya je ne domin ya samu ta fadi gasassa. Wadannan matsaloli ne suka janyo har yanzu ba a kai ga tantance manoma na gaskiya ba balle har a kai ga basu rancen.
.
Wata matsalar kuma, kamfanonin da za su tsayawa manoma su samu wannan bashin suna fargabar halin mutanenmu wajen iya murguda kudi ta hanyar da suke bukata. Wannan ta sa da yawan kamfanonin da ake kira 'Off Takers' suka ki amincewa da rattaba hannu a takardar yarjejeniyar. To amma a wannan makon mun ji cewar gwamnatin jihar Kano ta amince ta tsayawa manoman jiharta bisa sharadin za a kafa kotu ta musamman domin hukunta masu kunnen kashi.
.
Ga wanda yake bukatar wannan bashin har yanzu kofa a bude take, ana iya samu matukar an cike ka'idojin da aka tanada wadanda suka hada da:
- Bude asusu da Bankin Manoma
- Cikakken suna da adireshi
- Gona mai kimanin fadin kadada 1
- Lambar banki ta BVN
- Lambar waya mai aiki

Idan ka hada wadannan abubuwa, za ka iya zuwa kai daya ko a kungiyance zuwa bankin manoman da ke kusa da kai ka basu. Aikin tantancewa zai biyo baya. Haka kuma ana iya bi ta karkashin kungiyar manoma ta Nijeriya (RIFAN) wadanda za su shige maka gaba wajen samun wannan bashi cikin sauki.
.
Manoma sai a hanzarta samun wannan moriyar.

Alhamdulillah, Inna cikin wadanda suka anfana, sai fatan a taya mu add'ar iya mayarda su lapiya ,ya sanya mu anfana. Amma dai noman sai dai badi Idan Allah ya kai mu.
ReplyDelete