RIKITA - RIKITA
Labari daga
Danladi Haruna
Tun safe mata ke shiga suna fita, duk wadda ta shiga kuwa sai ta dade tana mamakin ganin irin wadannan dumbin kayan da aka zubo cikin wannan lefen. Babu shakka saurayin nan ya yi rawar gani, duk kyashi da kushe da hassadar mata 'yan gaza gani, ba su iya gano wata mishkila daga wadannan kayan lefen ba. Babu shakka komai ya ji.
Amarya Saude kuwa sai jiji da kai take tana wata irin tafiyar takama, jin kanta take kamar wata sarauniya tsakanin kawayenta. Su kansu kawayen tuni sun sallama mata, sun amince ta sha gabansu fiye da tsammaninsu. Duk unguwar nan tasu ba a taba samun budurwa ko bazawara da ta samu tumulin kayan lefe irin wannan ba. Saude kuwa da ake mata ganin 'yar gidan baya, babu wanda ya yi tsammanin za ta samu wani tagomashi na ku - zo - ku - gani. Wannan fa shi ne tsuntsu daga sama gasasshe, domin saurayin da ya zo bai wuce sati guda da ganinta ba, nan da nan kuwa aka kulla magana ta tashi daga karama zuwa babba.
Mata da yawa suna ta yake a fili gami da taya murna, suna cewa ashe ruwan ido ma yana da rana. Saude ta kasance yarinya mai tsananin ruwan ido da canki - canki tsakanin masu neman aurenta. Da yawa sun bayyana maitarsu a fili amma ta gwale su ta hanyar bula musu kasa a ido. Duk wanda ya fito sai ta kushe shi saboda bai mallaki wani abu da take so ba watau abin duniya. Burinta ta samu saurayi dan bana bakwai mai jini a jiki, ga katafaren gida da hamshakiyar mota gami da kadarori na ban mamaki. A nufinta ta yi auren da za ta rabu da fatara da talauci da babu. Ta ki jinin aikin da zai jawo ta wahala ko da za a samu wani abu matukar bai isa ta yi hidimar ta ta kimanin wata guda ba. Saboda haka daya bayan daya ta sallami duk masoyanta domin babu wanda take ganin ta dace da shi.
Bayyanar matashi Kashim ya juya mata tunani, ya sa ta gane ashe maza ma suna suka tara, ba duka ba ne matsiyata. Akwai masu kashin arziki, masu tashen arziki, masu rabon arziki da tinkaho da arziki. Ita kanta ta yaba da kasadar da ta yi ta hakura duk da korafin da ake yi mata na cewa ta ki fito da mijin aure saboda babanta ba ya duniya, sai ga shi a karshe jinkirin ya zama alheri. Domin a cewar ango Kashim, duk wani danginta ko wanda ya rabe ta ya rabu da talauci kenan har abada. Ya yi mata alkawarin duk wata zai rika kai ta wata kasa a cikin kasashen duniya domin ta kashe kwarkwatar idonta. Ya yi mata alkawarin ba ta hannun jari daga cikin abin da ya mallaka a kamfanoninsa. Babu shakka hausawa sun yi gaskiya da suke cewa cikin dare daya Allah kan yi bature.
Ango Kashim tun ranar da aka kawo kayan lefe ba a sake ganinsa ba, saboda wata tafiya ta kama shi zuwa kasashen waje. Duk da haka ya bayar da umarnin a ci gaba da al'amuran biki kada a fasa. Kowa na mamakin irin wannan dukiya da dan matashin nan ya mallaka, ga wani tafkeken gida ana gab da kammala aikinsa. Ga wata zundumemiyar mita mai sarrafa kanta sai ka ce kwamfuta. Motar na iya tuka kanta ta kai mutum inda yake bukata. Sannan za ta iya fada wa mutum irin matsalar da ke damunta da kuma yadda za a warware matsalar. Motar dai a takaice tana dauke da wasu ababen mamali na musamman. Sau biyu ta shiga motar nan ana yawatawa da ita cikin gari tana mamaki. Ango ya kara tabbatar mata da cewa da zarar an daura musu aure wannan motar ta zama tata.
Duk da a zahiri jama'a kowa na nuna farin cikinsa da gamsuwa da irin daular da Saude ke shirin afkawa, amma a boye da yawa na cike da kyashi da burin ina ma dai su ne suka samu ba ita ba. Wasu kuma cizon yatsa suke da suka ji labarin abin da ya yi sanadin haduwar ango da amarya kimanin sati biyu da suka wuce.
Ranar daurin aure ango bai samu halarta ba, amma dattawan nan da suka kawo kayan lefe a motar nan mai abin mamaki, su ne dai suka sake zuwa domin karbar auren. Tsoho mafi girman shekaru a cikinsu ne ya mika wata takarda ga liman yana fadin cewa, "ango ya yi tafiya zuwa Amirka, kuma daga nan zai wuce Landan da Jamus. Daga baya idan ya dawo ya huta zai dauki amaryarsa su tafi Saudiyya su yi Umara, sai ya kai ta kasar Dubai ta yi sayayya. Wannan sadaki ne ya bayar da caki a kawo muku."
Liman ya yi turus yana kallon 'yar takarda mai kunshe da wasu rubuce - rubuce da bai san ma'anarsu ba. Ya waiga ya dubi waliyin amarya ya ce, "ga takardar alkawari sun kawo. Me kuka ce?" Waliyin amarya ya ce, "alkawari kamar yaya?"
"Ina tsammanin sun bayar da takardar nan ne a matsayin kudin sadaki, idan Allah ya kaimu farkon mako a je a karbi kudin a banki." Wani mutum da ke cikin shaidu ya yi farat ya fada. Cikin sauri wakilin ango ya ce, "wannan haka yake, amma ku kaddara cewa kudin nan na hannunku. Domin a bankin da zarar an je kurum za a karba."
Waliyin amarya ya tsuke fuska ya ce, "to nawa ne kudin sadakin?" Wakilin ango ya ce, "miliyan daya da dubu dari biyar ne." Nan fa wuri ya kaure da hayaniya, jama'a suka hau tofa albarkacin bakinsu. Da yawa na fadin tun da suke ba su taba ganin an biya sadaki mai dumbin yawa irin wannan ba. Wasu kuwa nan take suka hau taradaddi suna inkarin wannan irin sadaki zururu kamar sayar da matar za a yi. Wasu na tsegumin wannan ango kuwa wacce irin sana'a yake yi da zai biya wannan sadaki haka?
Liman na rawar jiki saboda jin cewa shi ma an ba shi dubu dari na hadaya, waziransa an ba wa kowannen su dubu hamsin, kafin a kammala hayaniya tuni ya shiga karanta hudubar aure.
Sati guda da daura aure ango ya dawo daga tafiyar da aka ce ya yi kasashen waje. Ranar kuwa amarya ta tafi wurinsa domin gwajin takalmi kafin a yi taro na musamman na gagarumin biki wanda masu hasashe ke ganin za a jima ana tunawa da shi ta fuskar bushasha da bushasha.
Kasancewar ba a kammala warware wasu sabgogin biki ba ya sa amarya ba ta samu sukunin zuwa banki ta karbi kudinta ba. Kawunta wanda ya kasance waliyinta ya je da 'yar takardar da ake kira Cek zuwa bankin suka ce ba sunansa ba ne a jiki, wai dole sai sunan matar da aka rubuta a jiki ta kai kanta. Kuma sai ta zo da wata shaida da za ta nuna cewar ita ce wadda ake nufi.
Ango ya samu amarya a daidai, ya yi nishadi gwargwadon yadda zai iya domin amarya ta kasance cikin shiri na musamman yadda mijin zai ji ya kai matuka wurin samun biyan bukatunsa gare ta. Saude ba ta kasance cikin wata bukata da ta wuce irin daular da za ta fada ciki. Ta dubi katafaren gidan da tsinci kanta a ciki, an ce mallakar kanta ne. Ta tuna irin yadda rayuwa ta sha watangaririya da ita amma yanzu koma ya zo karshe. To amma abin da ya fi daure mata kai shi ne irin damuwar da angonta ya shiga na ganin sai ta zo da kayan lefen da aka kai mata baki daya. Ta yi mamaki yayin da ta ga ya zauna kan akwatunan yana dudduba kayan da ke ciki yana rubutawa. A tsammaninta so yake ya karo mata wasu kamar su. Abin da ba ta iya ganowa ba shi ne, angon nan rikici ya shiga maras misali ya auro ta.
Zan dora
Comments
Post a Comment