Kwana goma suna zaune cikin gidan da har yanzu ba ta iya zuwa ko kofar gida ba domin ko fita zai yi sai ya kulle ta daga ciki. A rana ta sha daya ya fita da zummar zai je duba takardar bizar tafiyarsu, ya bar ta tana tunani da kissime - kissimen abubuwan da za ta aiwatar a rayuwarta ta gaba. Sai ta ji ana kwankwasa kofa. Ta tashi zuwa kofar ta tsaya tana saurare har zuwa lokacin da ta ji an sake kwankwasa da karfi fiye da bugun baya.
"Wane ne?" ta fada cikin dari - dari
"Ku bude mana ku ga ko waye." Wata fusatacciyar murya ta fada.
"Wane ne?" ta fada cikin dari - dari
"Ku bude mana ku ga ko waye." Wata fusatacciyar murya ta fada.
Ta yi shiru tana tunani cike da fargaba. Ta ji dai muryar namiji mai alamun shekaru.
"Wa kake nema?"
"Ke Sabitu na nan? Ki ce masa ya bude Alhaji mai gidan ne?"
Ta ji wani abu ya tokare mata kirji kamar matokari. Ta hadiyi yawu da kyar sannan ta ce, "baya nan, ya fita." a zuciyarta kuma tana cewa, 'waye Sabitu, waye mai gidan?'
"To tun da baya nan, ki dan kauce gefe za mu bude da mukullin da ke wajenmu za mu shigo." Alhaji ya fada daga waje. Tana iya jin motsin wadansu mutanen, alamar ba shi kadai ba ne.
"Kamar yaya? Ta fada a razane
Kfin ta yi magana sai ta ji an zura mukulli daga waje ana kokarin budewa. Ta koma gefe guda ta rakabe ta zurawa sarautar Allah ido. A lokacin ta soma tunanin yaya za a yi babban gida irin wannan a ce babu maigadi, babu mai aiki, balle mai shara ko kula da shukoki. Ta tuna da irin tambayar da ta yi masa jiya ya ce, suna nan zuwa masu aikin saboda sun bata masa rai ne ya sallame su. Ta tuna yadda ya bararraje yana bata labarin rin dumbin dukiyar da ya ce ya mallaka da irin tanadin da ya yi mata. Idan kuwa gaskiya ya fada mata, to bai kamata wasu matsiyatan su zo su ce wai gidan nan nasu ba ne.
Bata ida tunani ba mutanen suka shigo, a kan wani gajeren mutum ne kakkaura, fuskarsa tafkekiya a murtuke kamar tasowar bakin hadari a farkon damuna. Biye da shi wasu firda - firdan karti ne su uku, kowanne ka dube shi za ka tabbatar da cewa sun dauko kamannin tsohon dan kokawar nan mai suna Hulk Hogan. Fuskarsu a murtuke irin ta ubangidansu, damatsansu marushi.
"Ke ce matar tasa?" Mutumin ya fada yana kallonta da jajayen idanunsa kamar rana za ta fadi a lokacin tsakiyar damina.
Ta ji jikinta ya kama rawa, harshenta ya hau karkarwa, ta kasa furta komai. Ya ci gaba da kallonta kamar mage da bera. "Yarinya kyakkyawa kuwa, ko a ina Haladu ya samo ta? Ba ta kamace shi ba." Ta yi sororo cike da tsoro tana jin abin da yake fada.
"Ina mijin naki ya tafi?" Ya tambaye ta daga bisani.
"Ya fita duba kayansa a airport." Alhaji ya bushe da dariya, sauran yaran ma suka tuntsure da dariya, yayin ita kuma ta sake nutsewa cikin duniyar tsoro da firgici da tunani. 'ni Saude na shiga uku, ga 'yan daukar amarya a gidana' ta fada a ranta cikin tsananin tsoro tana kallonsu suna dariya kamar tsofaffin aladun da suka kasa tafiya. A lokaci guda duk suka sha kunu, fuskokin suka koma kamar tsohuwar guzumar da yunwa ta yi wa kamun kazar kuku.
"Yarinya ta yaya kika san cewa mijinki ya tafi dubo kaya a airport? Wadanne kaya kenan? Ke dai ki fada mana gaskiyar inda yake babu abin da za mu yi miki, don haka ki saki jikinki kin ji." Ya mika hannu kamar zai taba ta. Ta yi hanzari ta matsa gefe guda jikinta ya ci gaba da bari kamar za ta saki fitsari. Ga shi ba ta nakalci fasalin gidan ba balle ta gudu ta buya, kuma tun da ta tare mijin bai yarda wani danginta ya zo gidan ba wai yana so ya kammala cin amarci tukunna. Ta ji kamar ta rusa ihu saboda ko wayar hannu ma babu a wajenta balle ta kira wasu ta fada musu halin da take ciki na wadannan muharramai har hudu a gabanta. Ba ta san abin yi ba.
"Ki kwantar da hankalinki," in ji Alhaji, ba za mu cutar da ke ba. Amma ina so na fada miki, mijinki Haladu ba shi da wasu kaya a airport, ban yi tsammanin ya ma ya san hanyar zuwa ba. Sannan kuma..."
"Ni fa ba sunan mijina Haladu ba, sunansa Kashim." Ta fada cikin karfin hali.
"Kina nufin ba shi ne wannan ba?" Alhaji ya nuna mata hoton mijin sanye da manyan kaya kamar irin wanda aka yi musu hoton murnar auren. Ta gyada kai ba tare da furta komai ba, zuciyarta na suya kamar an diga mata tafasasshen man gyada.
Ta ci gaba da tsurawa hoton ido tana numfarfashi kamar kirjinta zai fashe. Da alama Alhajin nan ya lura da halin da take ciki. Ya yi wani da guntun murmushi ya mikawa daya daga cikin kartin nan hoton. Ya maida kallonsa gare ta. "Yanmata babu wanda zai zarge ki yayin da kika mika wuyanki ga amincewa da auren wannan yaron. Na tabbata ba kyau ko asali kika duba ba, kin duba yiwuwar yana da mallakin masu gidan rana kamar ya tsara kuma ya yi nasara. Sai dai kuskurensa daya da ya manta har lokaci ya kure bai mayarwa da masu kayan da ya dauko haya abinsu ba. Wannan ne ya sa na tako da kafafuna domin na ji bahasi." Ya kalli daya daga cikin kartin nan ya yi masa alama da hannun. Katon nan ya matso gaba yana huci kamar kububuwa yayin da ta yi ido hudu da abokin gaba.
Muryarsa ta ratsa dodon kunnuwan Saude kamar rugugin aradu. "Sabitu Haladu ya zo wajen maigidanmu wannan ya karbi hayar gidan nan da motoci hudu tsawon sati biyu. Yau ya kara da kwana biyu akai, don haka muka zo mu fitar da shi dole. Tunda ba ya nan, muna so ki tattara naki ya naki ki fice daga gidan nan kafin lokaci ya kure ranmu ya baci." Rugugin muryarsa kadai ya sa kirjinta ya soma kunci, tsohuwar olsar da ke damunta ta soma barazanar dawowa sabuwa.
Ta dafe kirji tana mai sunkuyawa ba tare da sanin abin yi ba. Kanta ya soma hajijiya tana ganin wasu irin taurari kamar suna tsere a tsakaninsu, suna wuce ta gabanta da hanzari. Wasu shudaye, wasu jajaye wasu kuma bakake. Suka yi shiru suna kallonta har ta gama murkususunta ta mike idanunta jazur kamar gauta. "Ni fa ban sanku ba, ta yaya zan yarda da maganganunku. Idan ku barayi ne ku fito fili ku fada min ya fi wadannan bakaken maganganun da kuke fada min." ita kanta ta san ta yi cinikin taren aradu da ka da ta fada musu haka, sai dai ya fiye mata sauki akan ta bari a ranta yana konewa a banza.
Ba kamar yadda ta yi tsammanin za su mangare ta ko su yi mata aika - aika ba, sai ta ga Alhaji ya karbi faskekiyar wayar nan ya laluba wasu lambobi yana cewa, "kina da gaskiya, na tabbata bai fito fili ya fada miki irin aikinsa na wanke motocin sayarwa ba. Da kin san da haka da baki zarge mu da zuwa yi miki sata ba. Ina ma kudan yake balle romonsa?" ya bushe da dariya. Yaransa kuwa duk sun tsuke fuskokinsu suna mata kallo irin na mage da bera.
Ya kara wayar a kunne, lokaci kadan ya soma magana. "Please yaron nan fa baya gidan nan. Yaya za a yi?.... That very good, to a zo da shi yanzu yanzu... kai amma na ji dadin haka... to muna jiranku. Kar ku bata lokaci.. gara a sallami kyakkyawar yarinyar bana so ta shiga wani hali." Ya kashe wayar ya mikawa mai rikewa. Idanunsa na kallonta yana murmushi wani iri mai kama da kekkewa.
"Wadanda muka ba shi haya tare ne suka samo shi a wani wuri... ga su nan zuwa tare da shi za su karbi kayansu." Bata iya fadin komai ba ta durkusa cikinta na wani irin yamutsewa tana jin wani abu mai kama da yaukin miyar kuka yana mata karakaina tsakanin ciki da makogwaro.
Babu jimawa suka ji dirin mota, kafin a yi haka sai ga mutane hudu; biyu maza biyu mata. Mazan sun sa mijinta a tsakiya sun cukume shi yana zazzare ido kamar bera a buta. Rigar da ke jikinsa ta yi cidin - cidin sabanin rigar alfarmar da ya fita da ita. Ta daga kai ta kalle shi, sai mamaki ya kama ta yayin da ta ga ya kauda kai ba ya so su hada ido. To amma ita a zuciyarta so take ta gane wai shin da gaske wannan Kashim ne mijinta, ko kuwa wani ne mai suna Sabitu Haladu daban?
Tirka - tirka ta zafafa, kowa ya yi shiru yana kallon wani irin zance fasalin wasan kwaikwayo da ke gudana tsakanin miji da mata. Saude ta dube shi cikin mamaki da jirwayen fushi da gaurayen takaici ta ce, "me yasa ka kawo ni gidan da ba naka ba?"
Kai tsaye ya ce, "na fada miki ban karasa ginin gidan da za mu zauna ba ne." Jama'ar wajen suka kyalkyale da dariya. Ta bata rai ta ce, "kana nufin wannan gidan ba naka ba ne kamar yadda ka fada min?" Ya ce, "ba nawa ba ne, ga masu shi nan." A karo na farko daya daga wadanda suka cukumo shi ya yi magana ya ce, "Kuma kayan lefen da ya yi miki na aro ne." Daya daga matan ta ce, "wallahi kuwa, yanzu za a bamu kayanmu." Ta dubi mutumin da sauri sannan ta mayar da kallonta ga mijinta, wanda yanzu ya soma zame mata abin tsana maimakon abin so. Bai yarda sun hada ido ba kamar yadda ta so, ya sunkuyar da kansa yana mai cewa, "kar ki damu, idan na fita zan sayo miki wasu." Daya daga mutanen ya ce, "idan ka fita daga kurkuku ba. Kar ka ji da wai, idan aka duba aka ga tsinke ya bata a kayan nan, sai ka biya. Idan baka da kudi kuma ka yi zaman jarun."
Saude ta dube shi a hautsine, ta rasa abin da ke mata dadi, ta ji duk wani shauki so da kauna da yarda sun fita daga ranta. Maimakonsu tsana da kyama da fushi sun zauna. Bata da wani zabi face ta shake wannan matsiyacin kowa ya huta idan ya mutu. Sai dai jikinta babu kuzarin aiwatar da haka. A sanyaye ta jawo akwatunan da aka kawo lefen nan guda takwas ta ajiye gaban mutanen Suka shiga birkitawa suna karanta kayayyakin daga wata takarda suna dubawa. Can an jima matar ta dubi namijin da suke duba kayan tare ta ce, "babu atamfa uku 'yan holan da leshin siwiss da kuma 'yan ghana guda hudu." Mutumin ya ce, "sai a lissafa kudinsu ya biya kamar yadda aka yi alk'awari da shi." Saude dai tana rakube tana kallon ikon Allah yayin da Alhajin nan da yaransa ke zagaya gidan su ga an lalata musu wani wuri.
***** ***** *****
Rigima ba ta kare anan ba sai da ta kai an gurfanar da ango bisa tuhumar batar da kayan aro a gaban kuliya. Kodayake ya samu da kyar alkali ya amince da lamunin da ya dauka na cewar zai rika kawo wani abu duk karshe wata har ya gama biyan kudin kayan, to amma fa sai da ya je gidan maza tsawon wata biyu bisa horon gyara halinka.
Tuni Saude ta koma gida zaman jiran tsammani, domin ko ba komai dai ta riga ta zama karamar bazawara. Babban abin da take fargaba shi ne, kada a ce ta samu juna biyu da wannan gallababben da ya hana sakat cikin 'yan kwanukan da suka shafe a matsayin miji da mata. Ta sha alwashi ko ana ha maza ha mata sai ya bata takardar saki. A ganinta ma ko babu takarda auren ya riga ya baci tunda babu sadaki sai wata 'yar guntuwar takarda da aka je banki aka ce babu adadin kudin da aka bukata a cikin asusun.
Kawun Saude ya fi kowa shiga rikici da shan zargin wai bai yi bincike ba kurum ya shige gaba aka daura aure. Wasu har gori suke masa wai saboda ba 'yarsa ba ce ya sa shi aikata haka. Shi kuwa lokacin da suke walakiyarsu babu wanda ya neme shi sai daga baya. Duk wani bayani da yake yi wa mutane su fahimce ya zama a iska. Don haka ma ya hakura ya daina wani bayani dangane da zargin da ake masa.
Wata rana da yamma kawun Saude na kishingide yana sauraren rediyon Nijeriya na Kaduna cikin filin Tauraron Makada. A wannan ranar ana shakatawa ne da kidan kuntigi na Marigayi Danmaraya Jos. Duk da yana jin dadin launin kidan da wakar musamman yadda mawakin ke sassauya murya gwanin ban dariya, to amma a karkashin zuciyarsa tunanin yadda zai warware al'amarin nan cikin sauki yake yi. Shin kotu za su kai Kashim Sabitu Haladu a tilasta masa ya biya sadakin kuma ya saki 'yarsu, ko kuwa Allah ya isa za su yi masa? Shin yarinyar nan za ta yi hankali nan gaba ko kuwa za ta ci gaba da ruwan ido da kwadayi? Yaya zai yi wajen dawo da martabarsa wajen wadanda ke masa kallon biyu ahu alhali bai ji ba bai gani ba?
A daidai lokacin nan Danmaraya na rera wakar Dangaye, har an zo wurin da yake cewa,
Rikita - Rikitar Durun uwar nan,
An ba kuturu tukin mota,
Babu kwana ba jan birki,
Kai dan gaye ka kiyaye ni,
Domin ni ma na kiyaye ka,
Babu abin da ya dame ka,
Ni ma babu abin da ya dame ni....
Kawu yana jin wannan wajen sai ya daka tsalle ya ce, "kuma wallahi ni ne cikin Rikita - Rikitar nan. Amma daga yanzu babu abin da ya dame ni. Su je can su karata. Su suka siyo ko ma dai mene ne. Na janye hannuna!" Ya kade rigarsa ya shige gida.
KARSHE
Comments
Post a Comment