Watau har aka yi hawa da saukar $Sunusi ban san wainar da ake toyawa ba. Wannan kuwa na da alaƙa da jingine batun nazarin Cryptocurrency da na yi a gefe, musamman ganin ba duka ake wanyewa lafiya ba. Harka ce ta sai wani ya rasa wani ke samu. Faƙat.
Abu ɗaya da na fahimta, shi wannan bawan Allah da ya kawo sabgar, an shaide shi cewa mutumin ƙwarai ne ba zai zalunci mutane haka siddan ba. Haka kuma waɗanda suka shiga sabgar sun shiga da alwalarsu ne. Watau suna sane da kasadar da suka tunkara, suna cike da zummar idan ta yi kyau rijiya, idan ba ta yi ba masai.
To amma duk da haka wajibi ne a samar da cikakkun bayanai da hanyoyin da za a kiyaye aukuwar hakan nan gaba. Mazanarta za su so alkinta bayanan domin na gaba su ɗauki darasi.
Irin wannan abin da ya faru ga kuɗin kirifto na $Sunusi, a duniyar kirifto ana kiransa 'Rug Pull' ko 'Exploit'. Abubuwa da dama na jawo haka; na sakaci, da na rashin sani, har zuwa na ƙeta. A taƙaice, ga wasu 'yan shawarwari da jagorancin $Sunusi da masu dukiya a ciki za su iya bi domin samun nutsuwa, wanke kansu, da kuma kiyaye gaba:
1. Binciken Kwakwaf Mai Zaman Kansa (Verifiable Post Mortem Investigation)
Na ga cewar waɗanda abin ya shafa suna ta bayani a kan yadda lamarin ya auku, da lokaci, da hashes da sauransu. To ya kamata dukkan waɗannan bayanan a miƙa su ga ƙwararrun kamfanoni masu irin wannan binciken kamar Chainalysis ko Elliptic da sauransu. Hakan zai sake fitar da duk wani shakku na abin da ake kira 'Self Assessment' da ƙila wasu za su yi na zargin haɗin baki daga masu jagorancin $Sunusi. Kuma sun ƙara wanke kansu a idon duniya.
2. Daƙile Hanyoyin Fitar da Kuɗin Satar
A yi ƙoƙari a daƙile hanyoyin da ɓarayin za su iya fitar da kuɗin. Akwai hanyoyi da dama waɗanda masana da ƙwararru za su iya bi domin tare miyagun koda kuwa sun yi nasarar sacewa da karya darajar hajar. Misali, ana iya haɗa kai da kamfanoni kamar su Kraken, Coinbase, Binance da sauran wuraren musayar kuɗaɗe (CEX). Tun da sha'anin kirifto duk duniya ne, da zarar an sanar wa jami'an tsaro da dakarun kiyaye harkar kirifto na duniya, za su iya ɗaukar mataki nan take.
3. Sanarwa a Bayyane (Transparency)
Da zarar an samu wani bayani a sanar wanda zai kasance mutane na sane da irin ƙoƙarin da ake yi, da irin nau'in ɓarayi ko munafukan da suka haddasa wannan asara, watau 'infostealers'. Idan akwai wata ƙwayar cuta ta malware ko bug da aka samu, a bayyana ta yadda za a yi nazarin maganinta.
4. Shigar da Ƙorafi ga Jami'an Tsaron Cikin Gida
Yana da matuƙar muhimmanci a shigar da ƙorafi a hukumance ga hukumomin tsaro na gida (kamar sashen lura da laifukan intanet na 'Yan Sanda ko EFCC). Wannan zai bayar da damar bin diddigin duk wani ɓarawo da zai so ya karkatar da kuɗaɗen ta hanyar bankunan cikin gida wato P2P.
5. Ɗaukar Ma'auni (Snapshot)
Idan har akwai niyyar ci gaba da aikin nan, yana da kyau tawagar gudanarwa ta ɗauki bayanan yadda ma'aunin asusun kowane mamba yake (Snapshot) kafin aukuwar sacewar. Hakan zai sa al'umma su samu ƙwarin gwiwa cewa, idan abubuwa suka daidaita ko aka fitar da sabuwar Haja (V2 Token), za a iya mayar musu da abin da suka rasa ta hanyar 'Airdrop' ko 'Compensation'
6. Tantance Sabbin Hajoji (Smart Contract Audit)
A matsayin darasi na gaba, duk wata haja da za a fitar a gaba, ya zama wajibi a kai ta gaban ƙwararrun kamfanonin binciken kwakwaf na 'Smart Contracts' kamar su CertiK, ko Hacken domin su bincika ko akwai wata ƙofa (vulnerability) da ɓarayi za su iya bi kafin a saki hajar ga jama'a.
7. Ilimantarwa Kan Tsaron Asusun Kirifto (Wallet Security)
Kasancewar mutane da yawa sun shiga da alwalarsu, yana da kyau a saka musu shawarar kula da tsaron asusunsu (Wallets). A koya musu yadda ake cire izini (Revoking token approvals) a shafukan da ba su amince da su ba, ko amfani da 'Cold Wallets' don kiyaye kamuwa daga ƙwayoyin cutar intanet.
A ƙarshe, muna addu'a kuma muna miƙa kalaman jaje ga dukkan waɗanda suka yi asarar kuɗaɗensu a wannan iftila'i. Fatanmu Allah Ya mayar da mafi alheri, Ya kuma sa mu koyi
darasi daga abin da ya faru.

Comments
Post a Comment