Wannan muƙala tana yin fashin baƙi ne kan gagarumin tasirin da fasahar Basirar Na'ura (AI) ke da shi a fagen adabi da rubutun ƙagaggun labaran Hausa. Takardar ta yi bayani dalla-dalla kan yadda marubuta za su iya cin gajiyar manhajojin AI wajen inganta ayyukansu, wanda ya haɗa da sauƙaƙa gyaran ƙa'idojin rubutu, tsara tubalin labari, fassara zuwa manyan yarukan duniya, da kuma mayar da zallan rubutu zuwa sauti (audiobooks) don biyan buƙatar masu sauraro.
Haka zalika, takardar ta bayyana wasu manyan ƙalubalen da wannan fasaha ta taho da su. Musamman ta yi tsokaci kan barazanar gurɓata zantukan al'ada da falsafar Malam Bahaushe, da kuma sarƙaƙiyar matsalar haƙƙin mallaka (copyright) a ƙarƙashin dokokin Najeriya inda ta tabbatar da cewa rubutun da zallar na'ura ta yi ba ya samun kariya ta fuskar shari'a.
Wannan takarda tana da matuƙar muhimmanci ga kowane marubuci, ɗalibi, mai bincike, ko mai sha'awar adabin Hausa da ke son sanin yadda zai kiyaye asalinsa a yayin amfani da fasahar zamani.
👇 Latsa link ɗin da ke ƙasa domin sauke (download) cikakkiyar takardar a wayarka ko kwamfutarka:
Comments
Post a Comment